Ƴan Sanda Sun Hallaka Ɗan Ta’adda, Bayan Daƙile Harin Ta’addanci A Katsina
Ƴan Sanda sun yi nasarar hallaka wani ɗan ta’adda a jihar Katsina bayan da suka daƙile harin ƴan ta’adda a ƙauyukan Marina, da Garin Zaki, da Kadage, da kuma Ƴar-tsamiya dake a ƙarƙashin ƙananan hukumomin Safana da Batsari da Kurfi da kuma Musawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya na buƙatar 100,000MW domin magance matsalar wutar lantarki — Tsohon Minista
Kakakin Rundunar Ƴan Sandan Jihar, SP Gambo Isah ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis.
Ya ce a yunƙurin daƙile harin, jami’an ƴan sanda sun yi nasarar ceto mata uku da ƴan ta’addan sukayi garkuwa da su tare da gano bindiga ƙirar AK 47 uku da harsashi goma sha biyar da kuma babur biyu mallakin ƴan ta’addan.
Comments 1