Ƴar Shekara 70 Catherine Egbuche mace Mai buƙata ta musamman, tayi zaɓe, kuma ta bayyana cewa ta fito domin ta gudanar da zaɓe, duk da cewa har yanzu bata karɓi kuɗin sallamar taba, a matsayin ta na Ma’aikaciyar data ajiye aiki.
Tayi zaɓen a Makarantar Firamare ta Amaubia dake Amawbia a Jahar Anambra, ta shaida cewa, itace tafi kowacce mace farin ciki a faɗin duniya, duk da cewa tana da buƙata ta musamman.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓen Anambra: Masu kaɗa ƙuri’a suna zanga-zanga a Akwatin Soludo sakamakon matsalar da Card Reader ta samu
“Na fito domin in kaɗa ƙuri’a, Ina son mulki mai kyau. Miji na Makaho ne, amma kuma ina cikin farin ciki.
Na mai karɓar fansho ce, kuma ban karɓi garatuti na ba, amm Ina farin ciki, inji ta