Wani dalibi wanda ya rasa matsuguni ya yi matukar daukar hankalin mutane a kafafen sada zumunta bayan ganin ya koma kwana a ajinsu, Legit.ng ta ruwaito.
Wani dan makarantarsu wanda ya gan shi yana kwana a ajinsu kullum ne ya bayyana wa soshiyal midifya hakan inda ya ce zai tallafa masa.
KU KARANTA: Ƙungiyar asiri sun harbe ɗalibi har lahira a kwalejin Yabatech
Bayan kwashe awanni uku yana bacci ne aka gan shi a wannan yanayin wanda kowa sai da ya tausaya masa.
Kamar yadda dan makarantar nasu ya bayyana, ya ce a aji yaron yake kwana. Ya nufi wurinsa inda ya nemi ya taho tare da shi ya dinga kwana.
Sai dai abin banmamakin shi ne yadda ya ki amincewa da taimakon nasa inda ya ce ba ya don dora wa kowa dawainiya.
Matashin ya ce ya zo ya zauna da shi a dakinsu kasancewar wani dalibin da ke dakin ya tafi.
Sannan ya kuma nema masa tallafi a karshen bidiyon inda ya ce akwai kawunsa sa zai iya tallafa wa yaron ya biya masa kudin makaranta.
Sati 2 da ɗaukar ta aiki, an kama malamar makaranta tana ƙwazon gwada ɗalibinta a gado
Wata malama mai shekaru 22 tana hannun hukuma bayan an kama ta dumu-dumu ta yi lalata da wani dalibinta, LIB ta ruwaito.
Ashley Waffle, wata malamar wucin gadi a makarantar gwamnati ta Granite, ta fara aiki ne ranar 10 ga watan Oktoba, daga nan ta fara hira ta Snapchat da dalibinta mai shekaru 16 a ranar 25 ga watan Oktoba, wanda makwanni 2 kenan da fara aikinta.
Sai dai an samu labari a waje cewa jami’an makarantar sun sanar da ‘yan sanda abin da ke tsakanin Waffle da dalibinta bayan maganar ta fara yawa a gari.
Kamar yadda takardar kotu ta nuna, an ga waffle da yaron har sau biyu a dakinta kafin ranar 9 ga watan Nuwamba.