Wani mutum mai shekaru 34 Godwin Iroro ya shiga hannun dakarun rundunar ƴan sanda ta Ajegunle dake Jahar Lagos, sakamakon cin zarafin ɗiyar abokin sa da aka ɓoye sunan ta.
Wanda ake zargin an kama shine a ranar 25 ga watan Nuwamba na shekarar 2021, amma ya zargi shaiɗan da aikata wannan mummunan al’amari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Malawi: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Tsadar Rayuwa
An kama Iroro, biyo bayan ƙorafi da aka kai wajen ofishin ƴan sanda, wanda mahaifin yarinyar mai suna Chukwudi Chime yakai, wanda ya lura da abinda ya faru da ɗiyar sa.
Mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Lagos Adekunle Ajisebutu a cikin wata sanarwa, yace wanda ake zargin ya tabbatar da aikata lamarin, amma ya zargi shaiɗan da aikata hakan.
Sanarwar tace “ƙaramar yarinyar da lamarin ya faru da’ita, tace abokin mahaifin ta, dake zaune cikin gida ɗaya ya samu kwantawa da’ita a lokacin da mahaifinta bayanan a gida.
“Bincike ya nuna cewa dukkanin su basa tare da matan su, inda ita kuma tana tare da mahaifin ta.