Ɗan Takarar Gwamnan Osun ya fice daga PDP, bayan yasha Ƙasa
Wani Jigo a Jam’iyyar PDP a Jahar Osun Dr. Akin Ogunbiyi ya fice daga Jam’iyyar.
Ogunbiyi a ƴan kwanakin nan aka ka dashi a zaɓen Fidda Gwani na Gwamnan Jahar Osun a Shekarar 2022 a Jam’iyyar PDP.
KARANTA WANNAN LABARIN: Osinbajo Ya Taya Jagoran Jam’iyyar APC Tinubu Murnar Cika Shekaru 70 A Duniya
Ya bayyana cewar Dr. Iyorchia Ayu yana yin raɗin kansa a matsayin sa na Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar.
Dayake bayyana fitar da daga PDP a cikin wata takarda daya aikewa Ayu, ya godema Shugaban Jam’iyyar da irin yadda ya tattauna akan lamarin su na tsawon shekaru.