• Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli ta dage jadawalin karatu makarantar.
•Jiya laraba ne mahukunta Kwalejin su ka tabbatar da dage jadawalin bayan taron da suka gudanar.
• Daliban makarantar Sun nuna bacin ran su dangane da wannan lamari.
Mahukunta Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zaria, sun tsawaita jadawalin gabatar da aiyukan karatun Kwalejin, na shekarar 2019 da shekarar 2020. a jiya Laraba.
An saki sabon jadawalin ne bayan taron da mahukunta Kwalejin su ka gudanar, a sashin gudanarwa na makarantar.
Lokacin da ya ke karin haske dangane da sabon jadawalin, Dakta Umar Tabari daya daga cikin ma’aikatan Kwalejin, ya ce an dauki matakin ne, bisa rashin karasa karatu da mafi ya waicin sashin Kwalejin basu kammala ba, wanda kuma ya hadar da rufe makarantar, na kwana goma da aka yi a baya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar yan sandan ta baje kolin mutun 15
Kazalika hakan ya sa an dage zana jarabawar makarantar, zango na 2, 4, da na shida 6, da ta shiya gudanar wa, kwanaki kadan kafin fara wa.
A zantawar da gidan radiyon Kwalejin, ya yi da wasu daliban makarantar, Sun nuna bacin ran su, dangane da dage jadawalin, inda su ka ce, kudin daku nan, da su ka biya zai kare ne a wannan watan, kuma basu da kudin da zasu sake biya wani.
Comments 1