Daga: Abbas Yakubu Yaura
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ba shi da wani dan takara da ya fi so a zaben 2023.
An ga tsohon shugaban ne a wata ganawa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da yayi a birnin Landan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Benue Ta Kawar Da Fargabar Barkewar Cutar Amai Da Gudawa A Fadin Jihar
Wasu majiyoyi sun ce tsohon shugaban na Najeriya yana matsawa takarar Obi.
Amma da yake magana a Minna, babban birnin jihar Neja, a lokacin da ya kai wa tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubakar ziyara a ranar Lahadi, Obasanjo ya ce yana da wata manufa ta kasa, ba ta dan takara ba, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
“Ba ni da wani dan takara na musamman, ina da wata manufa ta kasa…. Na zo ganin dan uwana wanda ba shi da lafiya. Na yi shirin in ziyarce shi tun yana Landan, amma ranar da na isa Landan ita ce ranar da ya dawo gida.”
“Don haka ne na yanke shawarar zuwa na gan shi a gida. Shi na musamman ne don haka sai na zo.”
Abdulsalami ya mika mulki ga gwamnatin farar hula ta Obasanjo a shekarar 1999, wanda ya kawo karshen mulkin soja.
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Ƙaddamar da Munanan Hare-hare a Ƙananan Hukumomi 3 Na Jihar Katsina
‘Yan bindiga suna ci gaba da mayar da rayuwar mazauna jihar Katsina cikin wani mummunan hali, inda suka kai hare-hare da dama a fadin jihar cikin sa’o’i 72 da suka wuce.
A hare-haren da aka kai tsakanin Alhamis da Asabar, an sace wasu yara yayin da aka kashe iyayensu.