Daga: Abbas Yakubu Yaura
Jami’an ‘yan sanda a jihar Legas sun kama wani Andy Edwards da ya bayyana kansa a matsayin Kyaftin na Sojojin Najeriya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Bani Da Wani Dan Takara Dana Fi So, Cewar Obasanjo Bayan Ganawarsa Da Abdulsalami
“Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wani kaftin din soja na bogi, Andy Teddy Edwards, mai shekaru 39 da haihuwa da laifin fashi da makami.
“Sojan na jabu, wanda ya fito a matsayin mai yin tallan kayan kawa, zai gayyato mata ne domin tantancewa kayan sannan kuma ya yi musu fashin motoci da dukiyoyinsu da bindiga,” in ji Hundeyin.
PPRO ya kara da cewa, “An kama shi ne bayan wani bincike mai zurfi da aka gudanar bayan daya daga cikin wadanda abin ya shafa ta kai rahoton fashin da aka yi mata na motar Lexus RX330 SUV.
“Binciken da aka yi ya kai ga gano wata mota Ford Edge SUV mai lamba KRD 276 EG, injin dinki daya, na’urar cirar kudi ta POS guda daya mai katin SIM guda shida, kakin soja guda biyu, lambar mota guda daya – AFL 469 GD, a gidan wanda ake zargin.”
“Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, an bukaci mai Ford SUV da ya fito don yin ikirarin haka. Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya idan aka kammala bincike.”
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Legas, CP Abiodun Alabi, fdc, ya sake tabbatar wa mutanen jihar Legas irin jajircewar da jami’an tsaro ke yi na kawar da miyagun laifuka da aikata laifuka a jihar.”
A wani labarin kuma Gwamnatin Benue Ta Kawar Da Fargabar Barkewar Cutar Amai Da Gudawa A Fadin Jihar
Gwamnatin Binuwai ta kawar da fargabar da mazauna yankunan jihar ke da shi kan bullar cutar amai da gudawa a fadin jihar, tana mai cewa jami’an kiwon lafiyarta sun shirya tsaf don fuskantar kowane irin yanayi.
Babban sakatare na ma’aikatar lafiya da albarkatun dan adam, Dakta Terna Kur, a wata zantawa da Daily Trust ta wayar tarho a karshen mako, ya yi watsi da jita-jitar barkewar cutar a mai da gudawa a jihar.