By Abbas Yakubu Yaura
Wani tsohon shugaban majalisar dattawa, Cif Ken Nnamani, ya bayyana dalilin da ya sa yake neman ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Najeriya na gaba a 2023.
Sanatan yace dalilan da suka sanya nake son gaje kujerar Buhari shine domin samar da ingantaccen shugabanci da walwalar jama’a ga kasar.
Nnamani ya yi wannan jawabi ne a karshen mako a lokacin da yake jawabi ga gamayyar kungiyoyin matasa da magoya bayansa a shiyyoyi shida na siyasar Najeriya, wadanda suka zo ofishin yakin neman zabensa da ke Abuja.
Ya kara da cewa sun zo nan ne domin nuna goyon bayansu ga burinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa dan neman samun nasara.
Sanata Nnamani ya ce “idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai hada kan kasar nan, ya zurfafa dimokaradiyyar ta zuwa ga tudun muntsira”.
Sannan yace “zai sake gina hanyoyin zamantakewa da tattalin arziki don samun ci gaba mai dorewa da kuma rarraba damammaki da albarkatu a shiyyoyin siyasar Najeriya”.
Ya kuma tabbatar da cewa Nijeriya a halin da take ciki a yanzu; tana bukatar shugaban da aka gwada kuma amintacce tare da irin nasarorin da ya samu na dimokuradiyya a babban ofishinsa da ya gabata a kasar a matsayin sa na shugaban majalisar dattawa.