By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa zaben Matawalle bai samu wata hamayya ba.
FCTA Ta Sake Bude Kasuwar Sayar Da Kayayyakin Gini Ta Dei-dei
An tattaro cewa wakilai 735 da aka zabo daga gundumomin siyasa 147 na kananan hukumomin jihar 14 da suka halarci zaben duk ya samu amincewar su.
Babagana Tijjani-Banki, shugaban kwamitin zaben fidda gwani na gwamna a lokacin da yake bayyana Matawalle a matsayin wanda ya lashe zaben, ya ce daga cikin wakilai 735, kuri’u 733 sun samu sahihin zabe.
Tijjani-Banki ya yabawa wakilan da suka nuna dattijantaka da kuma kyawawan halaye a lokacin zaben.
A wani labarin kuma wasu ‘yan takarar gwamna uku a jam’iyyar PDP a jihar Zamfara sun koka da yadda zaben fidda gwani na jam’iyyar yake gudana
Yan takarar Ibrahim Shehu wanda aka fi sani da Shehu Bakaoye da Wadatau Madawaki da Hafiz Nuhuche, sun ce sun janye daga takarar ne sakamakon rashin bin ka’ida da Ake yi a zaben fidda gwanin.
A wata ganawa da manema labarai na hadin gwiwa da suka yi a Gusau, babban birnin jihar, mutanen uku sun yi zargin cewa sun lura da wasu kura-kurai wajen gudanar da zaben fidda gwani da suka ce ya tilasta musu janyewa daga zaben, tare da neman gyara ta hanyar da ta dace.
Sun ce za su kai karar jami’an dake gudanar da zaben ga hedikwatar jam’iyyar ta kasa domin a yi gyara.