Kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Yakubu Danladi-Salihu, ya yi kira ga gwamna Abdulrahman Abdulrazaq da ya bayyana aniyarsa ta neman wa’adi na biyu a hukumance.
Kakakin majalisar ya bayyana haka ne a karamar hukumar Moro yayin taron masu ruwa da tsaki a ranar Talata.
Kiran na zuwa ne kwanaki uku bayan shugaban jam’iyyar APC na jihar, Prince Sunday Fagbemi, ya bayyana cewa gwamnan zai iya tsaya wa takara a zaben shekarar 2023.
Shugaban majalisar ya ce lokaci ya yi da gwamnan ya kamata ya bayyana aniyarsa ta karo na biyu a hukumance, inda ya kara da cewa masu ruwa da tsaki a jihar Kwara ta Arewa a shirye suke su mara masa baya.
Kakakin majalisar, wanda shi ne dan jihar mai Matsayi na uku, ya bayyana aniyar tsayawa Takarar Gwamnan jihar da wasu a zaben shekarar 2023 da ‘yan siyasan yankin ke yi a matsayin iwu bayan hari.