Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi takama da cewa ba za a samu magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da za su kai 200 ba, don yin tattakin da zai yi.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita, yayin da yake mayar da martani ga wani sako da wani @ZamarOmar ya wallafa a shafinsa na Tuwita, wanda ya rubuta “Mutane miliyan biyu a Kaduna ga Peter Obi”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kenya Na Daf Da Fitar Da Sakamakon zaɓen Shugaba, Fafatawa Ta Yi Zafi Tsakanin Yan Takara 2
Gwamnan ya yi kamar ya yi wa ’yan kabilar Ibo ba’a yana mai cewa “masu shigo da kaya” wadanda ba sa iya bude shagunansu a ranar Litinin.
El-Rufai ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “A Kaduna? Ba Twitter Kaduna ba? – Ina fatan za ku sami mutane ɗari biyu a kan tituna, gami da waɗanda ‘masu shigo da kaya’ waɗanda ba za su iya buɗe shagunan su a ranar Litinin ba kuma sun zo cikin bas a cikin daren jiya!
“I jus’ dey laff, wallahi tallahi!!”.
Tuni dai aka gudanar da tattaki kan titi don Obi, inda aka samu adadi mai yawa a Nasarawa da Calabar.
A wani labarin kuma Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Edo sun ceto mutane 33 da aka yi garkuwa da su, ciki har da wani yaro dan shekara uku, yayin da wasu biyar sukayi batan dabo.
An tattaro cewa wadanda iftila’in ya afkawa na tafiya ne daga Agbor zuwa Benin a lokacin da wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Chidi Nwanbuzor, ya ce ‘yan sandan sun samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun fito daga cikin daji a kan titin Agbor-Uronigbe-Obiaruku inda suka yi awon gaba da wata motar bas Toyota Hiace da ta taso daga Agbor zuwa Warri suka shiga cikin dajin da su.
Ya ce wadanda ke cikin motar ‘yan kungiyar kwallon kafa ta Itugbe Kings, Warri ne a jihar Delta.
“Rundunar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji, ‘yan banga da kuma tawagar ‘yan sandan jihar Delta da ke kan iyakar jihar sun tattara tare da karade cikin dajin wanda ya yi sanadin kubutar da mutane 32 daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su a ranar 13 ga watan Agusta.
Ya ce yayin da ake bayyana wadanda abin ya shafa, an gano cewa har yanzu wasu biyar suna tare da masu garkuwa da mutanen, inda ya kara da cewa ana ci gaba da karade dajin domin ceto su.
Nwanbuzor ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga a wani harin sun kai hari kan wasu mutane biyu a cikin wata mota kirar Toyota Corolla da ta taso daga Bayelsa zuwa Agbor.
Ya ce duk da cewa sun tsere, daya daga cikin mutanen, Ibegu Daguapu, wanda aka harbe shi a kafadarsa ta dama, yana karbar magani a wani asibiti.