Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gabanin zaben 2023, jam’iyyar NNPP, ta sha alwashin karbe mulki daga hannun jam’iyyar PDP a jihar Enugu.
Shugaban jam’iyyar na jihar Enugu, Dr. Tony Ngene ya bayyana hakan a yayin wani taron koma-baya na kwana daya/ wayar da kan masu kada kuri’a da aka shirya wa daukacin ‘yan takararsu da shugabannin kananan hukumomi na jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’ar Sufurin Jiragen Sama Zata Fara Rajistar Daukar Dalibai – Sirika
Dokta Ngene, ya jaddada bukatar ci gaba a kan alfanun sabuwar dokar zabe wadda a cewarsa ta kara ba jama’a ikon zabar shugabanninsu wadanda suke so.
Ya tunatar da mahalarta taron cewa jam’iyyar NNPP ba jaririya ba ce a fagen siyasar Najeriya, yana mai jaddada cewa wani dan kabilar Igbo ne ya kafa jam’iyyar a matsayin dandalin gina sabuwar Najeriya.
“Dole ne mu ci gaba da samun karbuwar farin jinin jam’iyyar NNPP da kuma shugabancin mai girma daga tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso wanda shi ne ya fi kowa cancantar kafa sabuwar Najeriya a yankin Kudu maso Gabas musamman jihar Enugu.”
“Jagorancin yanzu kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabi’u Musa Kwankwaso yana tsaye a yau don yada wannan hangen nesa na gina sabuwar Najeriya wanda ba kawai zai yi aiki ga kowa ba, amma Najeriyar da za mu yi alfahari da ita,” in ji shi.
Shi ma da yake nasa jawabin, dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar da ke wakiltar Enugu ta Arewa Farfesa Onyeke Onyeke, ya ilmantar da ‘yan takarar kan sabbin al’amuran siyasar kasar nan, inda ya nuna damammakin jam’iyyar da kuma yadda jam’iyyar za ta yi amfani da damarta ta hanyar bin kowadanne ka’idojin dimokuradiyya.
Farfesa Onyeke wanda kuma farfesa ne mai ritaya a fannin kimiyyar siyasa, ya jaddada muhimmancin jajircewa, sadaukarwa da hangen nesa don amfanin jam’iyyar da daukacin al’ummar jihar.
Taron ya samu halartar daukacin ‘yan takarar jam’iyyar a jihar, shugabannin kananan hukumomi na jam’iyyar, da dukkan jiga-jigan jam’iyyar na jiha da wakilai daga ofishin jam’iyyar da ke Abuja, ya kasance tamkar wani motsa jiki ne na ilimi.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: NCAA Ta Dage Dakatarwar Da Ta Yiwa Kamfanin Jiragrn Saman Azman
Kamfanin jiragen sama na cikin gida na Najeriya, Azman Air, ya koma aiki bayan sabunta lasisinsa da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA tayi.
Kamfanin jirgin ya sabunta lasisin zirga-zirgar jiragen sama bayan dakatar da aikinsa a ranar Alhamis, da Hukumar NCAA ta yi, biyo bayan karewar takardarsa, ciki har da rashin biyan bashi.