An Jibge Jami’an tsaro a wurin Zaɓen Fidda Gwanin PDP na Lagos
Jami’an tsaro a ranar Laraba, an Jibge su a wurin da ake gudanar da zaben fidda gwani na Gwamna a Jam’iyyar PDP domin zaɓen Dan Takarar Gwamna a Jahar Lagos.
Kamfanin Dillancin Labaru na Najeriya ya bada rahoton cewa taron yana gudana a Cocin Cathedral dake GRA Ikeja.
An Sanya Jami’an tsaron a hanyoyin shiga da dama a farfajiyar wurin.
An hangi motoci Faturon da Tankoki a manyan hanyoyin da zasu kai mutum wurin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masari ya raba Filayen wanda Aikin Faɗaɗa Filin Jirgin Saman Umaru Musa ya shafa
Jami’an tsaron dake wurin sun haɗa da Ƴan Sanda, da DSS, da Ƴan Sibil Difens, da masu gadi da sauran su.
Dayake jawabi da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa, wani daga cikin Deliget Fatai Shodimu yace yana saran za’a kammala taron cikin kwanciyar hankali ba tare da samun hatsaniya ba.
Shima da yake jawabi, Samsudeen Arobieke ya bayyana fatan shi na kammala taron cikin kwanciyar hankali da lumana.
NAN ta bada rahoton cewa masu zaɓen fidda gwanin ana saran zasu fara daga ƙarfe 10 zuwa ƙarfe 2:00 na rana.
Mambobin Kwamitin Zaɓen wanda zasu gudanar da zaɓen har yanzu basu zo ba, suna jiran a tantance su.
PDP tana gudanar da zaɓen Jahar domin zaɓar Dan Takarar Gwamna domin Babban zaɓen Shekarar 2023 a Jahar Lagos.
NAN ta bada rahoton cewa, Ƴan Takarar Gwamna guda 6 ne ke yin Takarar da suka haɗa da; Ade Dosunmu, sa Olanrewaju Jim-Kamal, sa Gbadebo Rhodes-Vivour, sa Olajide Adediran, sa Adedeji Doherty, da kuma David Vaughan
Comments 1