A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da tsoffin gwamnoni jihohin Rivers da Kaduna, Nyesom Wike da Nasir El-Rufai a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa dake Abuja, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
A cewar jaridar, Wike ya isa gidan gwamnatin ne da misalin karfe 1:40 na rana, yayin da El-Rufai ya shiga bangaren shugaban kasa na Aso Rock da misalin karfe 2 na rana.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Gombe Ta Dauki Ma’aikatan Lafiya 260 Aiki
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa duk tsoffin gwamnoni biyun Wike da El-Rufa’i sune wadanda aka nada a matsayin ministoci
Yayin da Majalisar Dattawa ta tantance Wike kuma ta tabbatar da shi, El-Rufai har yanzu ba a wanke shi ba kan wani rahoton tsaro da ake jira.
Akwai rade-radin cewa ana kokarin ganin majalisar dattawa ta tabbatar da Malam El-Rufai.
A wani labarin kuma, Mallakar Makami: Emefiele Ya Fara Wani Yunkurin Dakatar Da DSS Daga Cigaba Da Gurfanar Da Shi
Shugaban CBN da aka dakatar, Godwin Emefiele ya bar babbar kotun tarayya da ke Ikoyi, Legas a ranar Talata, 25 ga Yuli, 2023, yana daf da shiga motar DSS da ke jira duk da umarnin kotu na bayar da belinsa tare da bayar da umarnin daina tsare shi a gidan yari.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, da aka dakatar, ya bukaci wata babbar kotun tarayya da ke zama a Legas ta dakatar da gwamnatin tarayya daga ci gaba da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin mallakar bindiga da alburusai ba bisa ka’ida ba ko kuma kan wani laifi makamancin haka.
Yana kuma neman umarnin kotu da ta sanya a daina tuhumarsa da dukkan laifuffukan da Gwamnati ta gabatar, kan rashin yin biyayya da bada belinsa a ranar 25 ga Yuli, 2023.
Emefiele ya kuma bukaci a kara bayar da umarnin haramtawa FG ci gaba da cin gajiyar duk wani nau’i na cin hanci da rashawa daga kotuna sai dai in har ba ta bi hukuncin belin ba.
Ta bakin lauyoyinsa karkashin jagorancin Babban Lauyan Najeriya, Joseph Daudu, Gwamnan CBN da aka dakatar ya shigar da karar a gaban Mai Shari’a Nicholas Oweibo wanda ya amince da bayar da belinsa bayan an gurfanar da shi a gaban kuliya.