Shugaban kungiyar ‘yan jaridu na jihar Yobe kwamared Rajab Mohammed, ya bayyana cewar da akwai bukatar kulla dankantar aiki tsakanin kafafen yada labarai da hukumar kula da safaran miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA .
Shugaban ya baiyana hakan ne a yayin da kungiyar ta NUJ ta kai wa kwamandan hukumar na jihar Yobe ziyarar bangirma a offishin su dake hanyar Gujba a Damaturu.
KARANTA WANNAN: Sabbin Manufofin Kasuwar Canjin Kudade Tsohon Labari ne, CBN ya Magantu
Shugaban kungiyar ta NUJ yace samun kawancen aiki tsakanin kafafen yada labarai da hukumar kula da safarar miyagun kwayoyi zai taimaka wajen kawar da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa a cikin jihar.
Kwamared Rajab Mohammed ya jaddada wa hukumar NDLEA cewa kungiyar zata bada dukkan goyon baya domin samun lafiyayar al’umma.
Ya kara da cewar kofar kungiyar a bude take domin wayar da kan al’umma a fadin jihar.
Tun farko da yake magana, kwamandan hukumar ta NDLEA din A.K Ogungboye yace hukumar a shirye take da tayi kwance da kafafen yada labarai domin wayar da kan al’umma kan illar miyagun kwayoyi.
Kwamandan ya kuma jaddada wa al’umma jihar musamman matasa da su nesanta kansu ga ta’ammali da miyagun kwayoyi domin samun lafiyar al’umma.
Ogungboye yace hukumar ta fito da wani sabon shiri da zai hada da shugabanin al’umma, shugaban addinai, da sauransu.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa a yayin ziyarar kwamandan hukumar ta NDLEA ya nada shugaban kungiyar ‘yan jaridu kwamared Rajab Mohammed a matsayin jakadan yaki da miyagun kwayoyi.
A wani labarin kuma, Duk Da Najeriya Na Da Girma, Ni Ba Za Ta Yi Man Wahalar Sarrafa Ta Ba – Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce aikin kiyaye Najeriya a matsayin ƙasa daya ne shine a gabansa, yana mai jaddada cewa kalubalen da ke ci gaba da cusa al’ummar kasar nan cikin mawuyacin hali na wucin gadi ne.
Da yake magana a yayin gabatar da wani littafi mai suna “Brutally Frank”, wanda tsohon ministan yada labarai, Edwin Clark ya rubuta a ranar Alhamis a Abuja, Tinubu ya ce Najeriya na da sarkakiya, amma ba ta da wahalar iya sarrafa wa.