- Kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya, JUSUN, reshen jihar Osun, ta fara wani mataki na masana’antu na sai baba ta gani
- Yajin aikin na zuwa ne biyo bayan zanga-zangar da JUSUN reshen Osun ta yi a ranakun Litinin da Talata kan Wasu bukatu
- JUSUN ta umurci dukkan ma’aikatan shari’a a jihar da su kaurace wa kotuna da ofisoshinsu su janye ayyukansu Nan take
Kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya, JUSUN, reshen jihar Osun, ta fara wani mataki na masana’antu na sai baba ta gani ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban kungiyar JUSUN na jihar Oluwagbenga Olakunle Eludire ne ya ayyana yajin aikin a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN: Kotun Daukaka Kara ta Sanya ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Nasarawa
Yajin aikin na zuwa ne biyo bayan zanga-zangar da JUSUN ta Osun ta yi a ranakun Litinin da Talata kan zargin rashin gudanar da mulki da ake yi wa babban alkalin Osun, Mai shari’a Oyebola Adepele Ojo.
‘Yan kungiyar ta JUSUN sun kuma zarge ta da cin zarafin wasu ma’aikata da kuma hana su hakkokinsu da suka hada da dawo da atisayen horaswa da basussukan alawus alawus din tufafi daga shekarar 2021 zuwa 2023 da kuma mayar da ma’aikatan shari’a a jihar da mai shari’a Adepele Ojo ya dakatar.
“Ya kamata a aiwatar da tsari da motsa jiki ba tare da bata lokaci ba.
“Haka kuma sauran fa’idojin da ‘yan kungiyar ta JUSUN suka cancanci a yi su ba tare da bata lokaci ba.”
Eludire ya umurci dukkan ma’aikatan shari’a a jihar da su kaurace wa kotuna da ofisoshinsu su janye ayyukansu.
A wani labarin kuma, Sojoji Sun Ceto Mutane 31 da Aka Sace a Sokoto
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta shiyyar arewa maso yamma Operation HADARIN DAJI sun ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su
Tuni sojojin suka tarwatsa maboyar barayin inda suka ranta Ana kare
Ceto Mutane ya biyo bayan kai Wani simame da dakarun Soji suka kai
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta shiyyar arewa maso yamma Operation HADARIN DAJI sun ceto mutane 31 da aka yi garkuwa da su a yankuna daban-daban na jihar Sokoto, a ranar Talata.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X ranar Laraba.