- Gwamnan Ribas Sim Fubara, ya kira taron gaggawa da mambobin ‘yan majalisar zartarwar jihar
- Gwamnan jihar shine wanda ya gaji, Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Wike, sun yi takun-saka kan tsarin jam’iyyar a jihar
- Gwamnan ya kiran taron ne biyo bayan ficewar ‘yan majalisar wakilai 27 Daga cikin 32 na PDP mai mulki zuwa APC
Gwamna Sim Fubara na jihar Ribas, ya kira taron gaggawa da mambobin ‘yan majalisar zartarwar jihar.
Taron na gudana ne a gidan gwamnati dake Fatakwal, babban birnin jihar.
KARANTA WANNAN: Dalilan da Suka Sanya Aka Samu Karancin Naira a Najeriya — CBN
Fubara ya yi kiran taron ne biyo bayan ficewar ‘yan majalisar wakilai 27 Daga cikin 32 na jam’iyyar PDP mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta APC.
‘Yan majalisar sun sauya sheka daga PDP zuwa APC a yayin zaman majalisar.
An ga ‘yan majalisar suna daga tutocin jam’iyyar APC a wani hoton rukuni bayan kammala zaman majalisar.
Fubara shine wanda ya gaji, Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Nyesom Wike, sun yi takun-saka kan tsarin jam’iyyar a jihar.
A wani labarin kuma, Dalilin Da Yasa Ba Ni da Group na WhatsApp Tare da Messi, Neymar – Suarez
Tsohon dan wasan gaba na Barcelona, Luis Suarez ya bayyana dalilin da ya sa ba ya Cikin group na Whatsapp tare da Tsoffin abokan wasansa Messi da Neymar
‘Yan wasan uku suna daya daga cikin manyan ‘yan wasan da aka fin tsoro a tarihi a lokacin da suke tare a Barca
Dan wasan ya zura kwallaye 26 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 17 a wasanni 53
Tsohon dan wasan gaba na Barcelona, Luis Suarez ya bayyana dalilin da ya sa ba ya da group na Whatsapp tare da Tsoffin abokan wasansa na Blaugrana Lionel Messi da Neymar.
Suarez, tare da Messi da Neymar, suna daya daga cikin manyan ‘yan wasan da aka fin tsoro a tarihi a lokacin da suke tare a Barca.