Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin a Maiduguri ya kaddamar da motocin bas masu amfani da iskar gas 107 da kuma motocin haya a kashi na biyu na shirin sufuri na metro na Gwamna Babagana Umara Zulum.
Shirin na nufin rage tasirin janye tallafin man fetur.
Karanta nanDa Dumi-Dumi: Gwamnan Ribas Fubara Ya Kira Taron Gaggawa Bayan ‘Yan Majalisa 27 Sun Koma APC
An gudanar da bikin kaddamar da motocin ne a kusa da fadar Shehun Borno amma kafin taron, shugaba Tinubu tare da rakiyar Zulum, sun kai ziyarar ban girma ga Shehu Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-kanemi.
Shugaba Tinubu ya je Maiduguri ne domin taron shekara-shekara na babban hafsan sojin kasa na bana, amma ya dauki lokaci wajen kaddamar da motocin Zulum, bayan ya ziyarci Shehu.
Gwamna Zulum a nasa jawabin a wurin kaddamarwar ya ce,mai girma shugaban kasa, bayan da ka sanar da cire tallafin da kuma umarninka ga gwamnoni na samar da agajin gaggawa, a jihar Borno mun yanke shawarar saka hannun jari sosai a tsarin zirga-zirgar jama’a.
An mayar da kowacce daga cikin motocin guda 107 zuwa amfani da wutar lantarki da iskar gas domin samun damar amfani da makamashi mai rahusa da kuma samar da sufuri mai arha ga ‘yan kasar wadanda galibinsu ke farfadowa daga barnar da rikicin Boko Haram ya yi fama da shi na sama da shekaru goma.
A wani labarin kumaGwamnatiin Jahar Kebbi Zata Inganta Albashin Ma’aikatan Lafiya A Jahar
Jihar Borno, a wannan shekarar, ta sayo motocin bas 120, daga cikinsu, Gwamna Zulum, a watan Satumba, ya kaddamar da motocin bas 77, wadanda aka aike da su sama da hanyoyi 15 a cikin babban birnin Maiduguri da karamar hukumar Jere.
Yayin da motocin zirga-zirga masu zaman kansu kamar Keke Napep karbar Naira N150 zuwa wani wuri motocin Zulum na karbar N50.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayan kaddamar da motocin guda 107 ya yabawa Gwamna Zulum bisa yadda ya samar da kyakkyawan shugabanci ga al’umma.