- A yanzu haka dai a wani Abu Mai kama da almara Linda Somari Stewart, daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ta yi wani Sabon sauyi
- Bayan sauya shekar tasu, kakakin majalisar dokokin jihar ya bayyana kujerunsu a matsayin wadanda babu kowa akan su
- Wannan ci gaban ya biyo bayan takun sakar dake tsakanin Wike da magajinsa, Gwamna Sim Fubara
A yanzu haka dai guda Cikin ‘yan Majalisun dokokin jihar Ribas 27 da Suka Sauya Sheka Suka Koma APC Linda Somari Stewart ta Koma gidanta na asali.
Stewart wanda ke wakiltar Okrika a majalisar dokokin jihar ta yi tariyar baya inda ta koma jam’iyyar PDP bayan ta sauya sheka zuwa jam’iyyar APC tare da wasu ‘yan majalisar.
KARANTA WANNAN: Aiyedatiwa Ya Koma Ondo a Matsayin Mukaddashin Gwamnan Jihar
Idan dai za a iya tunawa, ‘yan majalisar jihar su 27 da ake kyautata zaton suna goyon bayan Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Bayan sauya shekar tasu, kakakin majalisar ya bayyana kujerunsu a matsayin wadanda babu kowa akan su.
Wannan ci gaban ya biyo bayan takun saka tsakanin Wike da magajinsa, Gwamna Sim Fubara.
A wani labarin kuma, Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Shugabannin Hukumomin ICPC da FCSC
Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Dakta Musa Aliyu a matsayin kwararren shugaban hukumar ICPC bayan majalisar dattawa ta tabbatar da shi
A ranar 16 ga watan Oktoba, 2023, Tinubu ya nada shugaban hukumar tare da sakataren Hukumar ta ICPC
Sabon shugaban Hukumar ta ICPC Kafin nada shi ya rike mukamin Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Jigawa
Shugaban kasa Bola Tinubu a Ranar Laraba ya rantsar da Dakta Musa Aliyu a matsayin kwararren shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka masu alaka bayan majalisar dattawa ta tabbatar da shi.
Aliyu ya yi rantsuwar ne da misalin karfe 12:24 na rana a zauren majalisar zartarwa ta tarayya da ke Abuja.