- Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da Emmanuel John Echeofun, mashawarcin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abba Moro
- An dauke mashawarcin ga Shugaban marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa a kan hanyar sa daga majalisar dokokin kasar zuwa gidansa
- Kawo yanzu dai Shugaban marasa Rinjaye na Majalisar Dattawan Bai ce komai ba kan lanarin
An yi garkuwa da Emmanuel John Echeofun, mashawarcin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abba Moro.
An dai yi garkuwa da Echeofun ne a daren ranar Talata a kan hanyar sa daga majalisar dokokin kasar zuwa gidansa na Gwagwalada.
KARANTA WANNAN: Rikicin Ribas: Wata ‘Yar Majalisa Tayi Amai ta Lashe Bayan Sauya Sheka
Wata majiya mai tushe ta shaida wa DAILY POST cewa masu garkuwa da mutane suna neman kudin fansa naira miliyan 15 domin su sake shi.
“Sun ba mu har zuwa karfe 10 na safe yau don mu ba da kudin ko kuma su kashe shi,” Inji majiyar
A wani labarin kuma, Aiyedatiwa Ya Koma Ondo a Matsayin Mukaddashin Gwamnan Jihar
Mukaddashin gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya koma jihar, kwanaki biyu bayan ganawarsa da shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa dake Abuja
Wannan na zuwa ya yin da Mataimakin Gwamnan ya gana da shugaban kasa da wasu masu ruwa da tsaki kan rikicin siyasar jihar
Mukaddashin gwamnan ya isa jihar ne jim kadan bayan majalisar ta tabbatar da samun wata wasika daga gwamna Akeredolu da ke mika masa mulki
Mukaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya koma jihar ne a ranar Laraba, kwanaki biyu bayan ganawarsa da shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Aiyedatiwa ya gana da shugaban kasa da wasu masu ruwa da tsaki kan rikicin siyasar jihar Ondo.