- Victor Osimhen ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya da zakarun Serie A Napoli
- Dan wasan ya kafa kansa a matsayin daya daga cikin mafi kyawun dan wasan gaba a duniya
- Dan wasan ya zura kwallaye 26 a wasanni 32 da ya buga a lokacin da Napoli ta lashe gasar Scudetto a karon farko cikin shekaru 33
Victor Osimhen ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya da zakarun Serie A Napoli.
Osimhen ya sanya hannu kan kwantiragin shekara daya, wanda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2026.
KARANTA WANNAN: EPL: Merson Ya Yi Hasashen Yadda Wasan Liverpool,Arsenal da Man Utd Zai Kasance
An saki batun Biyan Kudin Wanda ya kai Yuro miliyan 130 a cikin sabon kwantiragin.
Har ila yau, dan Wasan gaban zai sami karin albashi mai tsoka.
Dan wasan na Najeriya ya koma Partenopei daga kungiyar Ligue 1 a shekarar 2020.
Dan wasan mai shekaru 24 ya kafa kansa a matsayin daya daga cikin mafi kyawun dan wasan gaba a duniya.
Dan wasan ya zura kwallaye 26 a wasanni 32 da ya buga a lokacin da Napoli ta lashe gasar Scudetto a karon farko cikin shekaru 33 da suka gabata.
A wani labarin kuma,Gwamnan Kaduna Ya Rattaba Hannu a Kan Kudirin Kasafin Kudin Shekarar 2024
Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani ya rattaba hannu a kan kudirin kasafin kudin shekarar 2024 wanda ya kai tsabar Kudi Naira biliyan N458,271,299,477.66.
A Cikin Kasafin Kudin Ilimi shine wanda ya fi daukar kaso Mafi tsoka don Ganin duk wani dan Jiha ya Samu ilimi Mai Inganci
Gwamnan ya nemi goyon baya da hadin kan al’ummar jihar domin fara aiwatar da kasafin kudin
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani a ranar Juma’a ya rattaba hannu a kan kudirin kasafin kudin shekarar 2024 wanda ya kai tsabar Kudi Naira biliyan N458,271,299,477.66.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a ranar Litinin ne gwamnan ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 ga ‘yan majalisar domin amincewa da shi.