- Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Hadarin Daji, OPHD, sun ceto mutane 52 da aka yi garkuwa da su, a wani samame da suka kai
- Tuni aka kai wadan aka ceto zuwa asibiti don duba lafiyarsu kafin su sake haduwa da Iyalan su
- A yayin kai simamen Sojojin sun hallaka ‘yan ta’adda da dama
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Hadarin Daji, OPHD, sun ceto mutane 52 da aka yi garkuwa da su, a wani samame da suka Kai cikin nasara da hadin kai a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta shafinta na X, ta ce hakan na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a yankunan da suke da alhakin.
KARANTA WANNAN: Dan Wasa Osimhen Ya Rattaba Hannu Kan Sabon Kwantaraginsa da Napoli
Sanarwar ta ce an samu nasarar ne a ranar 22 ga watan Disamba, 2023, lokacin da sojojin suka fatattaki ‘yan ta’addan a kauyukan Saruwa, Kubuta, Gundumi, da dajin Bunwanga Gundumi a karamar hukumar Isa.
“A yayin farmakin, sojojin na OPHD sun ceto mutane 52 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kashe ‘yan ta’adda da dama.
“Wadanda aka ceto sun hada da maza 14, mata 32, da kuma yara 6 wadanda za a duba lafiyarsu, za a kuma mika su ga hukumomin da suka dace domin hada su da iyalansu,” in ji ta.
A wani labarin kuma, Gwamnan Kaduna Ya Rattaba Hannu a Kan Kudirin Kasafin Kudin Shekarar 2024
Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani ya rattaba hannu a kan kudirin kasafin kudin shekarar 2024 wanda ya kai tsabar Kudi Naira biliyan N458,271,299,477.66.
A Cikin Kasafin Kudin Ilimi shine wanda ya fi daukar kaso Mafi tsoka don Ganin duk wani dan Jiha ya Samu ilimi Mai Inganci
Gwamnan ya nemi goyon baya da hadin kan al’ummar jihar domin fara aiwatar da kasafin kudin
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani a ranar Juma’a ya rattaba hannu a kan kudirin kasafin kudin shekarar 2024 wanda ya kai tsabar Kudi Naira biliyan N458,271,299,477.66.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a ranar Litinin ne gwamnan ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 ga ‘yan majalisar domin amincewa da shi.