- Manajan gundumar Legas na Kamfanin Jirgin Kasa na Najeriya, Mista Augustine Arisa, ya ce shirin shugaban kasa na hidimar jiragen kasa kyauta a lokacin bukukuwan kirsimeti dana Sabuwar Shekara ya taimaka ga matafiya
- Wannan ya biyo bayan Umarnin Shugaban Kasa Tinubu na Zaftare Kudin Sufuri Don Saukaka Zirga-Zirga
- Tuni dai jama’a Suka Shirya tsaf Domin kwasar wannan ta gomashi na Shugaban Kasa Tinubu
Manajan gundumar Legas na Kamfanin Jirgin Kasa na Najeriya, Mista Augustine Arisa, ya ce shirin shugaban kasa na hidimar jiragen kasa kyauta a lokacin bukukuwan kirsimeti dana Sabuwar Shekara ya Bada taimako ga matafiya da yawa.
Arisa ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Legas ranar Asabar.
KARANTA WANNAN: Sojoji Sun Ceto Mutane 52 da Aka Sace a Jihar Sokoto
Ya kuma yabawa Gwamnatin Tarayya bisa yadda take tallafa wa talakawa a lokacin bukukuwan domin samun damar yin biki tare da ‘yan uwansu ba tare da biyan kudin sufuri ba.
Manajan ya ce, hukumar tana yin lodin fasinjoji 6002 a kullum a cikin jirgin kasa na Mass Transit (MTT) daga Legas zuwa Ijoko da kuma fasinjoji 1,250 a kan Standard Gauge.
Ya ce suna kuma daukar fasinjoji 362 kyauta a kullum a cikin jirgin kasa na Apapa zuwa Kajola Standard Gauge.
“Dukkan zirga-zirgar jiragen kasa kyauta ne ga zirga-zirgar fasinja daga Iddo zuwa Kajola, Iddo zuwa Ijoko, Kajola zuwa Apapa, Apapa zuwa Kajola, Legas zuwa Ibadan, da Ibadan zuwa Legas, safe da rana, tare da umarnin shugaban kasa.
“Muna cikakken bin umarnin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na yin tuki kyauta har zuwa ranar 4 ga watan Janairu, 2024,” in ji Arisa.
Ya ce suna gudanar da tafiye-tafiye Sau biyu zuwa da dawowa daga Legas-Ibadan da Apapa-Kajola kyauta a kowace rana, yayin da suke tafiya kawai daga Iddo-Ijoko da Ijoko zuwa Iddo kowace rana.
A wani labarin kuma, Dan Wasa Osimhen Ya Rattaba Hannu Kan Sabon Kwantaraginsa da Napoli
Victor Osimhen ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya da zakarun Serie A Napoli
Dan wasan ya kafa kansa a matsayin daya daga cikin mafi kyawun dan wasan gaba a duniya
Dan wasan ya zura kwallaye 26 a wasanni 32 da ya buga a lokacin da Napoli ta lashe gasar Scudetto a karon farko cikin shekaru 33
Victor Osimhen ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya da zakarun Serie A Napoli.
Osimhen ya sanya hannu kan kwantiragin shekara daya, wanda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2026.