- Tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar APGA ,Cif Mathew Avre Ombugaku, a jihar Nasarawa, ya koma jam’iyyar APC
- Jiga-jigan siyasar da suka sauya sheka sun samu kyakkyawar tarba a jam’iyyar APC daga hannun shugaban jam’iyyar na kasa
- Taron sauya shekar ya samu halartar manyan kusoshin jam’iyyar
Cif Mathew Avre Ombugaku, tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar, APGA, a jihar Nasarawa, ya koma jam’iyyar APC a hukumance.
Sanarwar sauya shekar tasa ta zo ne a yayin wani liyafar karrama Sanata Solomon Aku Ewuga a ranar Asabar a dakin taro na birnin Lafiya.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kayode-Laguda Ya Samu Tikitin Takarar Kujerar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa
Ombugaku, tare da wasu jiga-jigan siyasa, sun samu kyakkyawar tarba a jam’iyyar APC daga hannun shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da Sanata Solomon Aku Ewuga.
Daga cikin fitattun mutanen da suka bi Cif Ombugaku wajen sauya sheka zuwa jam’iyyar APC akwai Dokta Alfa Yusufu Tsenya, tsohon dan takarar sanata a jam’iyyar APGA a Nasarawa ta Arewa; Aliyu Safiyanu, wanda aka fi sani da Mai Zuma, wanda ya kasance tsohon dan takarar majalisar wakilai ta SDP.
Sannan akwai Zubairu Abdullahi Musa da Musa Salihu Iyimoga, wanda ya wakilci mazabar Doma ta Arewa a majalisa ta 6 a dandalin ZLP.
Manyan baki da suka halarci liyafar sun hada da Gwamna Abdullahi Sule, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, Sanata George Akume, dan majalisar wakilai, Jeremiah Umaru, da wasu fitattun ‘yan siyasa.
A wani labarin kuma, Kisan Filato: Wasu Mata Masu Zanga-Zanga Sun Kone Gidan Wani Basaraken Gargajiya
Wasu fusatattun mata da suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da kashe-kashen da aka yi a jihar Filato sun kona gidan wani Hakimin
Zanga-Zangar fusatattun matan ta zone sakamakon kame wasu daga cikin al’ummar da ake zarginsu da hannu a kisan
Sai dai yadda zanga-zangar ta yi kamari ta kai ga isowar Jami’an tsaro wadanda suka tarwatsa masu zanga-zangar
Wasu fusatattun mata da suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da kashe-kashen da aka yi a wasu kauyuka a jihar Filato a ranar Juma’a, sun kona gidan Hakimin garin Bokkos, Michal Monday Adanchi.
Garin Bakkos da ke karamar hukumar Bokkos na daya daga cikin al’ummar da aka yi wannan kashe-kashen.