- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wani likitan bogi, Igwe Gift Okechukwu, da laifin hada baki, fataucin sassan jikin dan
- Wanda ake zargin ya kware wajen kulla alaka da mutane don ya cucesu inda takai ya damfari mai POS Zunzurutun Kudi Naira miliyan 21
- Tuni Rundunar ‘yan Sandan ta jaddada aniyar ta na yaki da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron al’umma
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wani likitan jabu, Igwe Gift Okechukwu, da laifin hada baki, fataucin sassan jikin dan, damfara, aikata laifuka ta yanar gizo, sojan gona da kuma satar katin shaida.
Jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta ‘yan sanda ne suka kama shi a jihar Nasarawa biyo bayan ayyukan damfarar wanda ake zargin a garin Owerri na jihar Imo.
KARANTA WANNAN: Nasarawa: Tsohon Dan Takarar Gwamna A Jam’iyyar APGA da Wasu Sun Koma APC
Wanda ake zargin, ya bayyana kansa a matsayin Henry Ovie, wani likitan kwakwalwa da aka mayar da shi zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC), Owerri, ya yaudari wata ma’aikaciyar hada-hadar Kudi ta (POS), Anita Chinwe Mathias, ta shigar da lambar a na’urarta ta POS.
Hakan ya sa aka cire gaba dayan zunzurutun kudi naira miliyan ashirin da daya (N21,000,000) daga asusunsa, lamarin da ya kai ga ta kai rahoton wajen ‘yan sanda.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya zayyana tsarin aikin wanda ake zargin, inda ya kulla amincewa da wanda iftila’in ya afkawa, ya aika da adadi mai yawa zuwa asusunsa, sannan ya yaudare ta ta shigar da lambar da ta taimaka wajen cire kudin ta hanyar yaudara.
A cewar Adejobi, Anita, wacce ta shigar da karar, ta bayyana cewa wanda ake zargin ya yi amfani da sunayen mutane da dama da kuma lambobin waya, inda ya bayyana a matsayin Igwe Richard da Ovie Henry.
“Ta ci gaba da bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2023, wanda ake zargin ya yaudare ta ta shigar da lambar a na’urar ta POS, wanda ta yi hakan ne saboda amincewar da ta yi masa.
“Bayan wanda ake zargin ya bar wurinta, sai ta lura cewa an cire dukkan kudaden da ke cikin asusunta na POS, wadanda suka kai naira miliyan ashirin (N21,000,000), kuma duk kokarin jin ta bakin wanda ake zargin ya ci tura.
“Ta kuma je Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, inda wanda ake zargin ya yi ikirarin yana aiki, domin ta tambaye shi game da shi, sai aka shaida mata cewa babu daya daga cikin Likitocinsu da ke da irin wannan suna, nan take ta kai karar zuwa sashin binciken manyan laifuka na Abuja. inda jami’an hazikan ‘yan sanda suka dauki matakin cafke wanda ake zargin,” sanarwar ta kara da cewa.
Bincike ya nuna cewa Likitan na jabu ya canza lambar wayarsa ya koma daga Owerri zuwa Lafiya ta Jihar Nasarawa, inda daga baya aka bi sawun sa aka kama shi.
An kuma gano cewa wanda ake zargin na da hannu wajen safarar sassan jikin dan adam, tare da alaka da wata hulda da ya yi a birnin Toronto na kasar Canada.
Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya jaddada aniyar rundunar na yaki da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron al’umma.
IGP din ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ana gudanar da bincike mai zurfi, kuma za a gurfanar da duk wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban kuliya.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Kayode-Laguda Ya Samu Tikitin Takarar Kujerar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa
Masanin harkokin kudi, kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, Fuad Kayode-Laguda, ya zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben cike gurbi
Wannan na zuwa ne bayan da INEC ta Sanya Ranar gudanar da Zabukan Cike Gurbi a wasu jihohin Tarayya
Dan Takarar Majalisar ya lashe zaben ne bayan samun nasara a zaben fidda gwani
Masanin harkokin kudi, kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, Fuad Kayode-Laguda, ya zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben cike gurbi na majalisar wakilai na mazabar Surulere 1.
Kayode-Laguda ya zama dan takarar ne ta hanyar lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar ranar Asabar a filin wasa na Teslim Balogun da ke Surulere a Legas.