- Gobarar daji da ta tashi a harabar kwalejin ilimi ta tarayya FCE ta lalata shaguna 10
- Lamarin da ya jefa wadanda lamarin ya rutsa da su cikin kunci, inda Gobarar ta yi awon gaba da miliyoyin naira
- Tuni dai mataimakiyar gwamnan jihar Farfesa Kaletapwa Farauta ta kai ziyarar gani da ido, inda ta gargadi Masu kona daji
Gobarar daji da ta tashi a harabar kwalejin ilimi ta tarayya FCE da ke Yola ta lalata shaguna 10.
Gobarar da ta afku a ranar Asabar ta yi sanadiyar kona daji.
KARANTA WANNAN: An Kame Likitan Bogi Da Laifin Safarar Sassan Jikin Dan Adam
Lamarin da ya jefa wadanda lamarin ya rutsa da su cikin kunci, inda suka koka da asarar kayayyakin da suka ce Gobarar ta yi awon gaba da miliyoyin naira.
Mataimakiyar gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa Farauta, wanda ta kai ziyarar gani da ido, ta gargadi mazauna yankin da su guji kona daji.
Ta ce: “Wannan shi ne lokacin rani. Iskar hunturun sanyi tana kadawa da ƙarfi sosai. Ya kamata jama’a su daina kona daji, musamman a kusa da wuraren zama.”
Daya daga cikin wadanda abin ya shafa mai suna Mercy Paul ta ce gobarar ta yi asarar dukkan kayan gyaran gashi da ta ke yi.
A wani labarin kuma, Nasarawa: Tsohon Dan Takarar Gwamna A Jam’iyyar APGA da Wasu Sun Koma APC
Tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar APGA ,Cif Mathew Avre Ombugaku, a jihar Nasarawa, ya koma jam’iyyar APC
Jiga-jigan siyasar da suka sauya sheka sun samu kyakkyawar tarba a jam’iyyar APC daga hannun shugaban jam’iyyar na kasa
Taron sauya shekar ya samu halartar manyan kusoshin jam’iyyar
Cif Mathew Avre Ombugaku, tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar, APGA, a jihar Nasarawa, ya koma jam’iyyar APC a hukumance.
Sanarwar sauya shekar tasa ta zo ne a yayin wani liyafar karrama Sanata Solomon Aku Ewuga a ranar Asabar a dakin taro na birnin Lafiya.