- Wata babbar kotun jihar Kaduna da ke zamanta a Kaduna ta yanke wa wani Idris Musa hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari
- Hakan ya biyo bayan kama wanda ake zargin ne a harabar wani banki dauke da katunan ATM na bankuna daban-daban guda 48
- Kafin cafke shi wanda ake zargin ya kware wajen iya damfara da musanya katunan ATM na wadanda basu ji ba basu gani ba
Wata babbar kotun jihar Kaduna da ke zamanta a Kaduna ta yanke wa wani Idris Musa hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari bisa samunsa da laifin damfara na ATM.
Kakakin Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, Dele Oyewale, shine wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar a Abuja ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN: Zaben Gwamnan Kano: ‘Yan Sanda Sun Yi Gargadi Da Babbar Muryar Kan Masu Tada Tarzoma
Oyewale ya ce mai shari’a A.A Bello ne ya yanke wa Musa hukunci a ranar Talata.
Ya ce wanda aka yanke wa hukuncin, wanda rundunar shiyyar Kaduna ta EFCC ta gurfanar da shi a gaban kuliya, ya amsa laifi guda daya da ya hada da damfara.
Tuhume-tuhumen guda daya ya ce: “Kai Idris Musa, wani lokaci a watan Yulin shekarar 2022 a Kaduna da ke cikin hurumin wannan kotu mai girma, ka yi wa wani Idris Ismail rashin gaskiya ta hanyar musanya katin ATM dinsa na bankin Zenith da sunan za ka taimaka masa ya ciro kudi, lamarin da ya yi sanadiyar gazawarsa. wanda ka san karya ne kuma ta haka ne ka aikata laifin da ya sabawa sashe na 306(a) na dokar jihar Kaduna ta shekarar 2017 da kuma hukuncin da ke karkashin sashe na 307 na wannan doka.”
Wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumar sa ne a lokacin da aka karanta masa kunshin tuhumar, wanda hakan ya sa lauya mai shigar da kara, M.U Gadaka ya roki kotu ta yanke masa hukunci.
Daga nan Mai shari’a Bello ya yanke wa Musa hukuncin daurin shekaru goma ko kuma biyan tarar N200,000.00k (Naira Dubu Dari Biyu kacal).
Tafiyar Musa zuwa Gidan Gyaran hali da tarbiyya ya fara ne a lokacin da aka kama shi da laifin musayar katin ATM na wadanda ba a san ko su wanene ba a kan zargin taimaka musu wajen sarrafa na’urar biyan kudi.
An kama shi ne a harabar wani banki dauke da katin ATM na bankuna daban-daban guda 48 a hannunsa.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu, Gwamnan Ribas Fubara Sun Shiga Ganawar Sirri a Villa
A halin yanzu dai shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan Ribas Simi Fubara
Zuwan nasa bai rasa nasaba da rikicin siyasar da ya barke tsakanin gwamnan da ministan birnin tarayya, game da mulkin jam’iyyar PDP a jihar
Wannan ya biyo bayan kara tsanani rikicin Siyasar jiyar inda aka wayi gari da murabus din shugaban Ma’aikatan Gwamnatin jihar
A halin yanzu dai shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas Simi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Gwamnan ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 5:35 na yamma. sannan ya wuce kai tsaye zuwa ofishin shugaban kasa.