- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya jajantawa iyalan wadanda harin bam ya rutsa da su a Ibadan
- Tuni dai gwamnan jihar kan lamarin ya zargi masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da haddasa fashewar
- Fashewar dai ta sanya tsoro a zukatan mazauna wurin da lamarin ya faru
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya jajantawa iyalan wadanda harin bam ya rutsa da su a jihar Oyo.
Ku tuna cewa fashewar ta faru ne da misalin karfe 7.30 na dare a Titin Dejo Oyelese dake Tsohuwar Bodija a Ibadan.
KARANTA WANNAN: Kwastam Ta Damka Katon Sama da 1k Na Jabun Magunguna Ga Hukumar NAFDAC
Gwamnan jihar, Seyi Makinde, a ranar Laraba ya zargi masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da haddasa fashewar.
Ya kuma tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu sannan wasu 77 sun jikkata.
Atiku a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X ya jajantawa gwamnatin jihar kan lamarin.
“Ina mika ta’aziyyata ga al’ummar jihar Oyo da gwamnatin jihar Oyo bisa fashewar wani abu da ya afku a babban birnin Ibadan da yammacin jiya Talata.
“Yayin da gwamnati ke ci gaba da bayar da tallafin jin kai ga wadanda fashewar ta rutsa da su, ina jajantawa iyalan wadanda ka iya rasa rayukansu da dukiyoyinsu sakamakon fashewar.”
A wani labarin kuma, Neja: An ceto Mutane 11, Takwas Sun Mutu, Wasu Sun Bace A Hatsarin kwale-kwale
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ta bayyana cewa, tawagar bincike da ceto na hukumar sun shiga aikin bayan mummunan hatsarin kwale-kwalen da ya afku
Wannan ya biyo bayan samu wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja a ranar Litinin
Kafin kifewar sa Jirgin fasinjan yana dauke da fasinjoji kusan 100 ya cika makil da mutane da kayayyaki
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ta bayyana cewa, tawagar bincike da ceto na hukumar tare da hadin gwiwar wasu masu ruwa da tsaki na cikin gida da suka tsunduma aikin cikin gaggawa da safiyar Litinin din data gabata bayan wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Borgu ta jihar.
A cewar Hukumar an ceto akalla mutane 11 da ransu, ya zuwa ranar Talata, 16 ga watan Janairu, 2024, an gano gawarwaki takwas (8) yayin da wasu 12 suka bace.