“Zan fi son komawa Babbar Ƙungiya, wacce za ta iya gogayya wurin cin kofi” – Ivan Toney
Ina so in taka leda a kulob din da ke fafutuka wajen neman lashe kofuna.
Ɗan Wasan gaba na Brentford Ivan Toney ya bayyana cewa yana son takawa wata babbar kungiya wasa a nan gaba.
A cewar Tony zai yi sha’awar tafiya zuwa kungiyar da ke nuna ƙwanji wajen ɗarewa a saman teburin Firimiya domin lashe kofin.
Ɗan wasan mai shekaru 27 zai koma buga kwallo a karshen makon nan bayan shafe watanni takwas na dakatarwar da akayi mashi.
Amma Tony wanda ƙungiyoyin Arsenal da Chelsea ke zawarci, bai yanke hukuncin barin filin wasa na Gtech Community Stadium ba wato Ƙungiyar Brentford.
KARANTA WANNAN LABARIN:Neja: An ceto Mutane 11, Takwas Sun Mutu, Wasu Sun Bace A Hatsarin kwale-kwale
Ya kuma faɗawa Sky Sports cewa”Ba za ku taɓa yin hasashen lokacin da na yanke don chanja sheƙa ba zuwa wata ƙungiyar ba, amma ina ganin a fili yake cewa ina so in taka leda a babban kulob.
“Kowa na son ya taka leda a babban kulob da ke fafutukar neman kambu, ko a watan Janairu ne lokacin da ya dace, ya kamata wani kulob ya shigo ya biya kuɗin da ya dace domin ɗauka ta? to ba wanda dai ya sani.
Amma babban abin da na fi mayar da hankali shi ne in cigaba da yin abin da nake yi a filin wasa, sauran kuma in bar magoya baya suyi aikin su.
A wani labarin kuma:Kwastam Ta Damka Katon Sama da 1k Na Jabun Magunguna Ga Hukumar NAFDAC
Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen jihar Sokoto, a ranar Laraba, ta mika katan 1,198 na magungunan jabu ga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa dake Sokoto.
Da yake jawabi yayin mika kayayyakin ga hukumar a ofishin shiyya na Sokoto, Kwanturola Musa Omale, ya ce kwacen ya yi daidai da manufar hadin gwiwa da babban Kwanturola Janar na Kwastam Bashir Adewale Adeniyi ya yi.