- Jam’iyyar APC reshen Osun ta ce soke zaben da Gwamna Ademola Adeleke ya yi na zaben da ya samar Sarakunan Gargajiya a jihar, ya kasance cin zarafi ne
- “Sa baki da gwamnan ya yi ba tare da wata bukata ba, sakamakon soke tsarin zaben da ya samar da Sarakunan wani mummunan aiki
- Wannan na Zuwa ne bayan da gwamnatin jihar ta ba da umarnin sake sabon tsarin zaɓe na cike gurbi sarakunan bayan da ta soke tsarin da aka samar da su
Jam’iyyar APC reshen jihar Osun, a ranar Juma’a, ta ce soke zaben da Gwamna Ademola Adeleke ya yi na zaben da ya samar da sarakunan Oba Adegboyega Famodun a matsayin Owa na Igbajo, ya kasance cin zarafi ne da siyasa.
A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Osun, ta ba da umarnin sake sabon tsarin zaɓe na cike gurbi sarakunan Aree na Iree da Owa na Igbajo, bayan da ta soke tsarin da aka samar da su tun da farko.
KARANTA WANNAN: Babu Gudu Babu Jada Baya Kan Korar Wasu Sarakunan Gargajiya Uku — Hadimin Gwamna
Gwamnatin ta kuma bayyana kujerar Akinrun na Ikirun, Oba Olalekan Akadiri a matsayin wanda babu kowa, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su jira a yanke hukunci kan kujerar da ke gaban kotun daukaka kara.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, Kolapo Alimi, ya fitar, ya bayyana cewa, matakin da gwamnati ta dauka a kan kujerun na kunshe ne a cikin takardun farar takardar guda shida a kan kwamitoci daban-daban da suka binciki batutuwan da umarnin zartarwa da gwamna Ademola Adeleke ya bayar a farkon taron gwamnati a watan Nuwamba 2022.
Adeleke dai ya sauya mukaman da magajinsa, Adegboyega Oyetola ya nada da nadin da aka yi wa daukacin sarakunan jihar a makwafinsa.
Ya kuma umurci Aree na Iree, Oba Ademola Raphael, Owa na Igbajo, Oba Gboyegba Famoodun da Akinrun na Ikirun, Oba Akadiri, da su bar fadar su tare da ba da umarnin gudanar da bincike kan hanyoyin da suka samar da su a matsayin sarakuna.
Jam’iyyar adawa a cikin wata sanarwa da shugabanta, Tajudeen Lawal ya fitar, ta ce sakamakon bita da kullin nadin sarautar Owa na Igbajoland, “rashin farin jini ne, zalunci, baje kolin cin hanci da rashawa da cin zarafi da ba za a iya gwadawa a shari’ar wasan wuta ba.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Abin mamaki ne yadda Gwamna Adeleke, duk da rashin amincewar karar, ya ci gaba da tauyewa Oba Famodun hakinsa wulakanci da kuma zalunci.
“Sa baki da Adeleke ya yi ba tare da wata bukata ba, sakamakon soke tsarin zaben da ya samar da Oba Gboyega Famodun a matsayin Owa na Igbajoland, wani mummunan aiki ne na wani mai shiga tsakani a cikin wani lamari da ke ci gaba da gudana a gaban kotu da rashin cancanta kuma mai wakilcin Gwamna Ademola Adeleke.
“Hanyar da Gwamna Adeleke ya yi kan batun da ake tafkawa ya saba wa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya wanda ya fito fili ya ba da damar raba madafun iko tsakanin bangaren zartarwa, majalisa da kuma bangaren shari’a.
“Gaskiyar magana ita ce soke tsarin zaɓen sarauta wanda ya biyo bayan tsarin da ya dace ba zai iya zama ba kuma ba zai iya tsayawa ba saboda wani sakamako ne na cin zarafi na siyasa.”
Da yake mayar da martani, mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed, ya ce Adeleke ya bi ka’ida, bin doka da al’adar garuruwa daban-daban da abin ya shafa a farar takardar.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: An Saki Tsohon Ministan Lantarki Daga Gidan Yari
Yanzu haka dai an saki tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye daga gidan gyaran hali na Kuje
Kafin sakin sa wata babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan a gidan kurkukun Kuje kan kwangilar dala biliyan 6
Aikin samar da wutar lantarki na Mambilla, wanda aka fara shi a shekarar 2003, ya sha fama da tashe-tashen hankula na shari’a da zargin cin hanci da rashawa
Yanzu haka dai an saki tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye daga gidan gyaran hali na Kuje bayan da ya cika sharadin belinsa.
Wakilinmu ya samu labarin cewa an saki Agunloye ranar Juma’a.