- Gwamnatin Yobe ta amince da bayar da kyautar Naira dubu N35,000 ga ma’aikatan gwamnati
- Bayar da kudaden ya kasance a matsayin wani tallafi na rage radadin wahalhalun da ake samu sakamakon cire tallafin man fetur
- Sakataren Gwamnatin jihar ya kasance shugaban kwamitin
Gwamnatin jihar Yobe ta amince da bayar da kyautar Naira dubu N35,000 ga ma’aikatan gwamnati a matsayin wani tallafi na rage radadin wahalhalun da ake samu sakamakon cire tallafin man fetur, Daily Trust ta rahoto.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban ma’aikata, Hamidu M. Alhaji, kuma aka mikawa sakataren gwamnatin jiha, Baba Malam Wali.
KARANTA WANNAN: APC ta Zargi Wani Gwamna da Cin Mutuncin Sarakunan Gargajiya
Takardar wadda ta ce Gwamna Mai Mala Buni ya amince da nadin sakataren Gwamnatin jihar a matsayin shugaban kwamitin kan bayar da kyautar Naira dubu N35,000 ga ma’aikatan gwamnatin.
Sannan ya kuma bayyana cewa kwamitin na da mambobi shida tare da Babban Sakatare Kaddamarwa a matsayin sakataren kwamitin.
Kwamitin zai tantance abin da ya shafi kudi na aiwatar da ba da lamunin albashi da kuma yin shawarwari da kungiyoyin kwadago kan kudaden da za a amince da su ga gwamnati da kungiyoyin.
A wani labarin kuma, Babu Gudu Babu Jada Baya Kan Korar Wasu Sarakunan Gargajiya Uku — Hadimin Gwamna
Mai magana da yawun gwamnan Osun, Olawale Rasheed, ya ce ba za a janye shawarar da aka yanke kan batutuwan da suka shafi sarauta a jihar ba
Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar ta ba da umarnin sake zabar sabbin kujerun sarakunan bayan ta soke tsarin da ya samar da su
Gwamnati ta tsaya tsayin daka kan matakin da aka dauka kuma ta na kira ga jama’a da su yi watsi ga duk wani rahoto da ya saba wa doka
Mai magana da yawun gwamnan jihar Osun, Olawale Rasheed, ya ce ba za a janye shawarar da aka yanke kan batutuwan da suka shafi sarauta kamar yadda yake kunshe a cikin farar takarda da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Alhamis ba.
Gwamnatin jihar Osun ta ba da umarnin sake zabar sabbin kujerun sarakunan Aree na Iree da Owa na Igbajo, bayan da ta soke tsarin da ya samar da su.