- Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, yanzu haka yana Abuja
- Sakataren wajen Amurka zai gana da shugaba Tinubu don tattauna muhimman batutuwa
- Duk da cewa yana rangadin Afirka, daga baya Blinken zai tashi zuwa Legas
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, yanzu haka yana Abuja, babban birnin Najeriya.
Blinken ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 4 na yamma, inda zai wuce fadar shugaban kasa ta Villa domin ganawa da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: DSS ta Kame Shugaban Miyetti Allah Bisa kafa Kungiyar ‘Yan Banga
Duk da cewa yana rangadin Afirka, daga baya Blinken zai tashi zuwa Legas da misalin karfe 10 na dare domin sauran al’amuran da aka shirya yi a gobe Laraba.
Bayan tattaunawar kuma ana sa ran gobe da daddare zai tashi daga Najeriya zuwa Angola.
A wani labarin kuma, PDP ta Dakatar da Shugabanta Bisa Zargin Almundahanar Naira Miliyan 19
An dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Dekina a jihar Kogi, Ibrahim Huseini
Ayyukan Shugaban sun kawo cikas ga ci gaban jam’iyyar ta hanyar kin bin tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar
Tsige Shugaban jam’iyyar ya samu taron dangi daga jiga-jigan jam’iyyar ta PDP
An dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Dekina a jihar Kogi, Ibrahim Huseini har sai baba ta gani.
Huseini, kafin dakatarwar da aka yi masa, an zarge shi da karkatar da Naira miliyan 19 daga asusun jam’iyyar da kuma yin barazana ga mambobin jam’iyyar.