- Jami’an Hukumar DSS sun cafke shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo
- DSS ta bayyana cewa an kama shugaban kungiyar ne saboda fargabar cewa kirkiro kungiyar ‘yan banga na iya haifar da tashin hankali a Najeriya
- kungiyar ba ta da rajista da Hukumomin tsaro, don haka gwamnatin tarayya ba ta amince da ita ba
Jami’an Hukumar DSS sun cafke shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, kan samar da kungiyar ‘yan banga a jihar Nasarawa.
An kama Bodejo ne a ranar Talata a babban ofishin Miyetti Allah, Tundun Maliya Cattle Market dake da tazarar Kilomita 22 da Babban Titin Abuja-Keffi, Tundun-Wada, cikin Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa.
KARANTA WANNAN: PDP ta Dakatar da Shugabanta Bisa Zargin Almundahanar Naira Miliyan 19
Jami’an DSS tare da wasu sojojin Najeriya, an ce sun kai farmaki babban ofishin Miyetti Allah da ke kusa da Cocin Goshen, da misalin karfe 3:40 na yammacin ranar Talata, yayin da suka tashi bayan kama Bodejo a kofar ofishin.
Wata majiya ta DSS da ta tabbatar wa wakilinmu kamen ta bayyana cewa an kama Bodejo ne saboda fargabar cewa kirkiro kungiyar ‘yan banga na Nomad’s na iya haifar da tashin hankali a fadin kasar nan.
Ya kara da cewa kungiyar ba ta da rajista da DSS, ‘yan sanda, ko wata hukumar tsaro, don haka gwamnatin tarayya ba ta amince da ita ba.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Jami’an (DSS) da sojojin Najeriya sun kai farmaki a ofishin Miyetti Allah da ke Nasarawa a yammacin yau, kuma mun kama shugabansu na kasa Bello Bodejo da ya kafa kungiyar ‘yan banga da Gwamnati ba ta san da ta ba.
“Kirkirar kungiyar ‘yan banga na makiyaya na iya haifar da tashin hankali a kasar. Kungiyar ba ta da rajista da DSS, ‘yan sanda, ko wata hukumar tsaro, kuma kungiyar gwamnatin tarayya ba ta amince da ita.”
Da aka tuntubi kakakin hukumar ta DSS, Dokta Peter Afunanya, bai amsa kiran waya da sakon tes da wakilinmu ya yi masa ba.
A halin da ake ciki, bayan kafa kungiyar ’yan banga, Bodejo ya jaddada cewa, ‘yan banga na sa kai za su bi ka’idojin da kasar ke da su a yayin gudanar da ayyukansu.
A yayin kaddamar da bikin a garin Lafia na jihar Nasarawa, Bodejo ya bukaci ‘yan banga na sa kai da su hada kai da ‘yan sanda, sojoji, da sauran jami’an tsaro domin ganin an samar da ingantaccen tsarin tsaro a fadin kananan hukumomi 13 na jihar Nasarawa.
A wani labarin kuma, Yadda Sabon shugaban Kasar Laberiya, Boakai Ya Kasa Kammala Jawabin Rantsar da Shi
Sabon shugaban Laberiya da aka rantsar, Joseph Boakai, ya gamu da cikas ba zato ba tsammani a yayin jawabin rantsar da shi
Damuwa game da lafiyar Boakai ya kasance babban batu a lokacin yakin neman zaben sa
Shugaban mai shekaru 79, wanda ya kwashe kusan mintuna 30 yana jawabi ga al’ummar kasar, sau biyu Yana tsayawa wanda hakan ya tilasta dage bikin
Sabon shugaban Laberiya da aka rantsar, Joseph Boakai, ya gamu da cikas ba zato ba tsammani a yayin jawabin rantsar da shi, wanda ya sa aka dakatar da bikin na wani dan lokaci.
A cewar BBC, shugaban mai shekaru 79, wanda ya kwashe kusan mintuna 30 yana jawabi ga al’ummar kasar, ya yi kokarin kammala jawabin nasa.