- Jam’iyyar APC reshen Akwa Ibom, ta ce ta tsaya tsayin daka kan ikirarin shugabanta, Sanata Godswill Akpabio
- Jam’iyyar ta yi watsi da martanin da jam’iyyar, PDP ta mayar, inda ta zargi shugaban Majalisar dattawa
- Ƴan jihar ba za su iya jiran zaben 2027 ya kawo karshen mulkin PDP a Jihar ba, kuma muna ba da tabbacin za mu samar da gwamnan jihar na gaba
Jam’iyyar APC reshen jihar Akwa Ibom, ta ce ta tsaya tsayin daka kan ikirarin shugabanta, Sanata Godswill Akpabio, na kokarin karbar mulkin jihar ta hanyar zabe a 2027.
Jam’iyyar ta yi watsi da martanin da jam’iyyar, PDP ta mayar, inda ta zargi Sanata Akpabio.
KARANTA WANNAN: Saudiyya Za ta Bude Kantin Sayar da Giya Na Farko A Babban Birnin Kasar – Rahoto
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, a wata sanarwa da ya fitar, ya bukaci Akpabio da ya fuskanci gaskiyar cewa jihar Akwa Ibom jiha ce ta PDP kuma babu wani “da’ ko makircinsa na karya” da zai iya canza halin da ake ciki.
Ologunagba ya shaida wa Akpabio da ya ba da karfinsa wajen tunkarar kalubalen da ke neman kawo masa cikas a matsayinsa na Shugaban Majalisar Dattawa, wanda a cewarsa, “ana zarginsa da aikata rashawa.”
Sai dai kuma Sakataren Yada Labarai na APC Iniobong John, a wata sanarwa mai taken “Ba wata farfagandar karya da za ta hana APC yin kokawa da mulki daga PDP a Akwa Ibom a zaben 2027.”
APC tace martanin da PDP ta mayar a Ranar Alhamis kan ikirarin Sanata Akpabio ya tabbata na tsoron gaskiyar da ke kasa ne
Da yake bayyana furucin na PDP a matsayin farfaganda, kakakin jam’iyyar APC ya ce jam’iyyar za ta yi amfani da duk wata halastacciyar hanya wajen yin kokawa kan mulki a zabe mai zuwa.
A cewarsa: “Tuni dai jam’iyyar PDP ta fara yada farfagandar karya a kan Shugaban Majalisar Dattawa, domin ‘yan Akwa Ibom ba za su iya jiran zaben 2027 ya kawo karshen mulkin PDP a Jihar ba, kuma muna ba da tabbacin za mu samar da gwamnan jihar na gaba.
“Abin da babban jagoranmu, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce, wato cin zaben 2027 a jihar ta hanyar halal, zaman lafiya da halal, shi ne abin da zai faru kuma babu wata farfagandar karya ta Debo Ologunagbas na wannan duniyar zai dakatar da shi.
“Wannan abun da Debo Ologunagba ya yi yana nuna rashin komai ne kawai, rashin iya aiki, karama da irin matakin da PDP ta taka.”
Ya shawarci Ologunagba da ya yi taka-tsan-tsan da yadda yake “yin amfani da ofishinsa wajen fitar da karya, yaudara, farfagandar da ba ta da tushe balle makama ga jama’a game da masu rike da mukaman gwamnati.”
A wani labarin kuma, Mun Shirya Tsaf Don Sake Gudanar da Zabe a Kano – ‘Yan Sanda, INEC
Rundunar ‘yan sandan Kano ta bayar da tabbacin a shirye ta ke ta samar da tsaro a zaben da za a sake gudanarwa a ranar 3 ga watan Fabrairu
“Mun tattara isassun jami’an tsaro da za su samar da tsaro kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe
“Duk mutumin da ba shi da katin zabe na dindindin ba zai shiga zaben da za a sake yi ba”
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayar da tabbacin a shirye ta ke ta samar da tsaro a zaben da za a sake gudanarwa a ranar 3 ga watan Fabrairu a mazabu uku na kananan hukumomi shida na jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Hussaini Gumel, ne ya bayar da wannan tabbacin ranar Laraba a Kano a lokacin da yake zantawa da manema labarai gabanin zaben.