An yanke ma Wata ƴar kasuwa Hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari bisa laifin Safarar ƴan Mata
Wata Babbar kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa wata mata Patricia Igbinovia ‘yar shekara 55 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samun ta da laifin safarar ‘yan mata zuwa ƙasashen waje domin yin karuwanci.
Kotun ta kuma umarci mai laifin da ta biya tarar kuɗi Naira Miliyan 1 bisa aikata laifin da ta aikata baya ga zaman gidan yarin.
Hukumar hana fataucin mutane ta NAPTIP ta kasa ce ta gurfanar da wacce ake tuhuma da laifin shida, da suka haɗa da safarar ƙananan yara, da mata domin yin karuwanci a gaban mai shari’a Chukwujekwu Aneke a gaban kotu.
Da take tuhumar, mai gabatar da kara, Mrs Becky Jibo ta ce wacce ake tuhuma da laifin na cikin wata kungiya da tayi shura wajen shiryawa tare da daukar nauyin fitar da ‘yan mata zuwa kasashen waje domin yin sana’ar karuwanci da lalata.
KARANTA NAN:Jihar Kebbi ta kori wasu hakiman gundumomi 3 saboda Zargin zamba
Ta ce wanda aka yanke wa hukuncin ta ɗauki ‘yan mata ne daga Jihar Legas zuwa Malaga a kasar Spain domin yin karuwanci.
Bayan da mai laifin ta amsa laifin da ake tuhumar ta da shi, mai gabatar da ƙara ya bukaci kotun da tayi duba akan laifin, inda Alkalin kotun ya amince da hakan.
Mai gabatar da ƙara ya kira wata mai shaida Misis Mabel Bajulaiye wata mamba ce a cikin tawagar da ta binciki bayanan sirrin Kungiyar masu aikata laifukan ta Najeriya.
Mai Shaidar ta shaida wa kotun yadda a shekarar 2016 Gwamnatin Tarayya ta hannun ofishin babban mai shari’a ta samu bayanan sirri game da wata kungiyar da ke safarar ‘yan mata zuwa Madrid da Malaga a kasar Spain.
Bajulaiye ya ce an sanya ‘yan matan yin karuwanci ne domin lalata da kuma samun kudi.
A cewar shaidar an gano laifin ne saboda hadin kai tsakanin gwamnatocin Najeriya da Spain kan safarar mutane da suke yi da nufin yin karuwanci.
A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Aneke ya ce ya saurari bukatar da masu laifin suka yi na neman a yi musu sassauci musamman ganin wadds ake tuhumar ba ta ɓata lokacin kotu ba wajen amsa laifin.