- Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya ce kofar jam’iyyar a bude take ga gwamna Abba Yusuf
- “Za mu samar da yanayi mai kyau ga duk wadanda suka sauya sheka don ci gaban siyasa da Dimokuradiyya
- Wannan na Zuwa ne bayan da aka jiyo Gwamnan Yana jinjinawa Shugaban Kasa Bola Tinubu da kuma yabawa kan hukuncin da kotun koli ta yanke da gaskiya
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya ce kofar jam’iyyar a bude take ga gwamna Abba Yusuf na jihar Kano.
Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Kano.
KARANTA WANNAN: PDP ta Amince da Hukuncin Da Kotun Koli ta Yanke Kan Zaben Gwamnan Sokoto
A cewarsa, “Ina kira ga Gwamna Yusuf, tare da mambobinsa na jam’iyyar NNPP, da su sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a matakin kasa domin tabbatar da ci gaban siyasar jihar.
“Muna kuma aiki tukuru don ganin ‘yan majalisar tarayya daga jihar Kano da sauran jam’iyyun siyasa sun hada kai da masu ci gaba domin kofofin jam’iyyar a bude suke ga kowa da kowa.
“Za mu samar da yanayi mai kyau ga duk wadanda suka sauya sheka don ci gaban siyasar jam’iyyarmu da jiharmu baki daya.
“Ina so in tabbatar wa mutanen jihar Kano nagari cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bullo da tsare-tsaren da za su inganta rayuwar al’umma.
“Ina kuma tabbatar muku da cewa akwai wani yunkuri na wasu gwamnoni daga jam’iyyun siyasa daban-daban su shigo jam’iyyar mu.
“Ba da jimawa ba wasu gwamnoni da ‘yan majalisar wakilai daga wasu jam’iyyun siyasa za su koma APC,” inji shi.
A cewarsa, jam’iyyar reshen jihar Kano ta amince da hukuncin da kotun koli ta yanke da gaskiya tare da jinjina wa shugaba Tinubu kan soyayyar da yake yiwa jam’iyyar.
Da yake bitar hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben Kano, Ganduje ya ce jam’iyyar za ta samar da wata hanya mai karfi da za ta hada kan mambobinsu tare da ba da dama ga mutane masu son shiga jam’iyyar.
Ganduje ya ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun kuma nuna godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu kan goyon bayan da yake yi wa Kano.
“Kofar jam’iyyar APC a bude take ta jawo sabbin ‘ya’yan jam’iyyar a fadin kasar nan da kuma kasashen waje a matakin kungiya ko daidaikun jama’a saboda kyakkyawan shugabanci da alkawurran da jam’iyyar ta dauka.
“Don haka, domin inganta hadin kai, ci gaba da ci gaban jihar Kano, taron masu ruwa da tsakin sun bayyana aniyar ci gaba da bin hanyar tattaunawa da daidaikun mutane, kungiyoyi ko jam’iyyun siyasa da ke shirye su koma APC,” inji shi.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tsare Mutane Biyar Masu Biyayya Ga Gwamnan Ribas Fubara
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin tsare wasu magoya bayan gwamnan jihar Ribas
Masu biyayya ga Gwamnan an tsare ne bisa zarginsu da hannu a fashewar wani abu da ya rutsa harabar majalisar dokokin jihar
Fashewar ta afku ne a daidai lokacin da wasu ‘yan majalisar suka yi yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Alhamis ta bayar da umarnin tsare wasu magoya bayan gwamnan jihar Ribas bisa zarginsu da hannu a fashewar wani abu da ya rutsa harabar majalisar dokokin jihar Ribas.
Wani fashewa ya afku a harabar majalisar dokokin jihar a daidai lokacin da wasu ‘yan majalisar suka yi yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara a ranar 30 ga watan Oktoba, 2023.