Kotu ta yanke wa wasu ‘yan banga biyar hukuncin kisa a Kano
A ranar Alhamis ne wata babbar kotu a Jihar Kano ta yanke wa wasu ‘yan kungiyar ‘yan banga biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutuwar wani yaro dan shekara 17.
Mutum biyar da aka yankewa hukuncin dai sun hada da Emmanuel Korau, da Elisha Ayuba, da Irimiya Timothy, da Auwalu Jafar da kuma Mustapha Haladu waɗanda ke aiki a cibiyar matasa ta Sani Abacha. Sun gurfana a gaban kotu kan mutuwar wani matashi mai shekaru 17 Ahmed Musa wanda aka kashe.
Lauyan masu gabatar da ƙara Barista Lamido Soron Dinki ya shaida wa kotun cewa waɗanda aka yanke wa hukuncin sun aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Janairun shekarar 2022 a ƙaramar Hukumar Sabon Titi Panshekara Kumbotso da ke Jihar Kano da misalin karfe 10 na safe bayan da suka haɗa baki suka kai wa marigayin hari a lokacin da ya ke wucewa ta hanyar Sabon Titin Panshekara.
KARANTA NAN:PDP ta Amince da Hukuncin Da Kotun Koli ta Yanke Kan Zaben Gwamnan Sokoto
A cewarsa “Waɗanda ake tuhumar sun fito ne daga cikin babur mai ƙafa 3 wato Napep, suka fara dukan mamacin da doguwar sandar katako, wanda ana cikin haka ne marigayin ya riƙe sandar kuma a sakamakon haka ya samu munanan raunuka wanda ya kai ga mutuwarsa.
Alkalin kotun mai shari’a Dije Aboki, ta ce lauyan masu shigar da ƙarar ya gabatar da shaidu biyar a gaban kotun tare da tabbatar da karar sa ba tare da wata shakka ba.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 97 da na 221 (b) cikin baka, na kundin laifuffuka.
Don haka mai shari’a Dije Aboki ta yanke wa waɗanda ake tuhuma su biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya.
A wani labarin kuma:An yanke ma Wata ƴar kasuwa Hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari bisa laifin Safarar ƴan Mata
An yanke ma Wata ƴar kasuwa Hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari bisa laifin Safarar ƴan Mata
Wata Babbar kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa wata mata Patricia Igbinovia ‘yar shekara 55 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samun ta da laifin safarar ‘yan mata zuwa ƙasashen waje domin yin karuwanci.
Kotun ta kuma umarci mai laifin da ta biya tarar kuɗi Naira Miliyan 1 bisa aikata laifin da ta aikata baya ga zaman gidan yarin.
Hukumar hana fataucin mutane ta NAPTIP ta kasa ce ta gurfanar da wacce ake tuhuma da laifin shida, da suka haɗa da safarar ƙananan yara, da mata domin yin karuwanci a gaban mai shari’a Chukwujekwu Aneke a gaban kotu.
Da take tuhumar, mai gabatar da kara, Mrs Becky Jibo ta ce wacce ake tuhu