- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a jihar Oyo ta tabbatar da tashin gobara a ofishinta
- INEC tace lamarin ba zai shafi sake zaben da za a yi a jihar ba
- A ranar 3 ga sabon wata ne INEC za ta Gudanar da zabuka a jihar
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a jihar Oyo ta tabbatar da tashin gobara a ofishinta dake karamar hukumar Ibadan ta kudu maso gabas.
Kwamishinan zabe na jihar, Dr Adeniran Rahmon Tella, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ya fitar a ranar juma’a.
KARANTA WANNAN: Gwamnan Ribas Fubara Ya Rantsar da Kwamishinoni Tara da Suka Lashe Amansu
Sannan ya bayyana cewa wutar ta tashi da misalin karfe 10:30 na safe.
Yayin da ya ke bayyana cewa ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ba, ya dage cewa lamarin ba zai shafi sake zaben mazabar Saki ta Yamma da ke Jihar ba.
“Babu wani rai da aka rasa sai kayan aikin da suka kone,” in ji shi, yana mai jaddada cewa lamarin ba zai shafi sake zaben mazabar Saki ta Yamma da ke tafe a ranar Asabar, 3 ga watan Fabrairu, 2024 ba.
A wani labarin kuma, 2027: PDP Ba ta Bukatar Yin Maja – Jigon jam’iyyar
Wani jigon PDP kuma tsohon mamba a kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Dr Adetokunbo Pearse, ya ce jam’iyyar ba ta bukatar wata maja
PDP ba ta mutu ba sai dai kawai tana bukatar ta rufe sahu domin ta ci zabe
“PDP ba za ta iya guduwa ba, mu manta da maja, shin kuna maganar hadewar PDP da wasu jam’iyyun siyasar da ba su da ofisoshi?
Wani jigon PDP kuma tsohon mamba a kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Dr Adetokunbo Pearse, ya ce jam’iyyar ba ta bukatar wata dunkulewa wato maja kafin zaben 2027.
Pearse, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Legas, ya yi watsi da yiwuwar hadewar jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun siyasa.