- Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya nada sabbin manyan sakatarori 13
- Nadin nasu ya zo ne bayan nasarar da sabbin wadanda aka nada suka samu a jarrabawar tantancewa
- Wannan ya kasance don cike guraben da ake da su a ma’aikatan jihar
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya nada sabbin manyan sakatarori guda 13.
Fintiri da yake bayyana wadanda aka nada a ranar Juma’a, ya ce ana bukatar su cike guraben da ake da su a ma’aikatan jihar.
KARANTA WANNAN: Ana Saura Kwanaki Ai Zabe, Gobara ta Tashi A Ofishin INEC Da Ke Ibadan
Ya ce nadin ya zo ne bayan nasarar da sabbin wadanda aka nada suka samu a jarrabawar tantancewa da Kwalejin Gudanarwa ta Najeriya ASCON ta gudanar, inda mutane 64 suka shiga.
Wadanda aka nada sun hada da Mundi Musa Ibrahim daga karamar hukumar Guyuk; Adama Mamman Karamar Hukumar Hong; Dogara Musa, Hong; Fabian Wambai, Jada; Oliver Gani, Lamurde; Abubakar Umar, Maiha; da Zira Bubanani Mathias, Michika.
Sauran sune Kwaji Duguri karamar Hukumar Michika; Ruth Huram, Michika; Makallan Akila, Song; Tanimu Buba, Yola ta Arewa; Heidi Edgar Amos, Yola ta Kudu da Muhammad Amin Suleiman, Yola ta Kudu.
Da yake jawabi tun da farko kafin bayyana sakamakon jarabawar, Gwamna Fintiri ya ce gudanar da jarabawar wata manufa ce ta gwamnati na karfafa ayyukan yi.
Ya kara da cewa jarabawar nadin manyan sakatarori da hukumar ta waje, ASCON ta gudanar, ita ce hanya mafi inganci wajen inganta tsarin da zai magance son zuciya wajen nada manyan sakatarori.
Shugaban ma’aikata na jihar, Isah Shehu Ardo, ya bayyana cewa sama da manyan ma’aikata 100 ne suka nuna sha’awarsu, daga cikinsu 64 da aka samu sun zana jarrabawar da aka gudanar a watan Nuwambar shekarar 2023.
A wani labarin kuma, Gwamnan Ribas Fubara Ya Rantsar da Kwamishinoni Tara da Suka Lashe Amansu
Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya kafa tarihi ranar juma’a a lokacin da ya rantsar da kwamishinoni 9
Wannan na Zuwa ne bayan da kwamishinonin a karo na biyu suka koma gwamnati bayan sun mika takardar murabus
Gwamnan ya ce da kwamishinonin ya zama wajibi su gudanar da ayyukan da zuri’a za su rika tunawa da su
Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya kafa tarihi a lokacin da ya rantsar da kwamishinoni 9 da ke komawa majalisarsa a karo na biyu bayan sun mika takardar murabus din nasu.
Kwamishinonin wadanda su ma a wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, sun yi murabus daga mukaman su baki daya a cikin watan Disamba saboda zazzafar rikicin siyasa a jihar Ribas.