- Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya kafa tarihi ranar juma’a a lokacin da ya rantsar da kwamishinoni 9
- Wannan na Zuwa ne bayan da kwamishinonin a karo na biyu suka koma gwamnati bayan sun mika takardar murabus
- Gwamnan ya ce da kwamishinonin ya zama wajibi su gudanar da ayyukan da zuri’a za su rika tunawa da su
Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya kafa tarihi a lokacin da ya rantsar da kwamishinoni 9 da ke komawa majalisarsa a karo na biyu bayan sun mika takardar murabus din nasu.
Kwamishinonin wadanda su ma a wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, sun yi murabus daga mukaman su baki daya a cikin watan Disamba saboda zazzafar rikicin siyasa a jihar Ribas.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokokin Ribas ta Kada Wata Kuri’a Kan Gwamna Fubara
A kwanakin baya ne majalisar dokokin jihar ta sake tantance su a wani yanayi na tarihi.
Sai dai kuma sake tantance su da kuma rantsuwar da suka yi a ranar Juma’a na daga cikin wa’adin zaman lafiyar shugaban kasa mai maki 8 da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa bangarorin da ke rikici da juna na Gwamna, Fubara da magabacinsa kuma Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.
Da yake gudanar da atisayen a zauren majalisar zartarwa ta Jiha da ke Brick House Port Harcourt, Gwamna Fubara ya shaida wa kwamishinonin da suka dawo cewa ya zama wajibi su gudanar da ayyukan da zuri’a za su rika tunawa da su.
Yayin da yake lura da cewa tuni sun karanta tuhume-tuhumen kamar yadda yake kunshe a cikin rantsuwarsu, Gwamna Fubara ya umarce su da su kiyaye da kuma kare kundin tsarin mulkin jihar.
Yace; “Ina muku fatan alheri a dawowarku. Ku tsaya kan adalci, mu tsaya kan muradun jiharmu. Dalilin nadin naku kenan da kuma gaskiya.
“Na ga yadda zukatanku suka yi nauyi. Amma ina tabbatar muku cewa ba ni da wani abu a kan kowannenku. An kama ku a tsakanin lokacin da ake tsaka da wuta.”
Gwamna Fubara ya ci gaba da cewa: “Zan ba ku shawara ku ba da mafi kyawun ku. Kamar yadda na fada a karon farko, bari wannan Jiha da ‘ya’yan baya su tuna da ku kan abin da yake mai kyau.”
A wani labarin kuma, ‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu da Ake Zargi da Sace Man Taransifoma
Rundunar ‘yan sandan Yobe ta sanar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin hada baki da kuma sata
An kama wadanda ake zargin dauke da jarkoki da bututun jan mai suna tsaka da kokarin yashe man
Masu laifin zasu fuskanci fushin doka da zarar an Kammala bincike
Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta sanar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin hada baki da kuma satar man dizal na taransifoma.
Sanarwar ta fito ne a cikin wani rahoton halin da ake ciki daga jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar, Dungus Abdulkarim, wanda aka rabawa manema labarai a Damaturu ranar Juma’a.