- Wani soja mai ritaya da wani farar hula sun shiga hannun jami’an jirgin ruwan Najeriya wadanda suke dauke da wani abu mai nauyin kilogiram 400
- Cafke masu laifin ya biyo bayan wani simamen da jami’an sojin ruwa suka kai
- NDLEA tace za a bincike su da kyau kafin a gurfanar da su gaban kuliya domin su zama masu hana wasu
Wani soja mai ritaya da wani farar hula sun shiga hannun jami’an jirgin ruwan Najeriya na Lugard, Lokoja, wadanda suke dauke da wani abu mai nauyin kilogiram 400 da ake zargin tabar wiwi ne a hanyar Ajaokuta zuwa Lokoja a jihar Kogi.
Mutanen biyu, Denis Foukorighe, soja mai ritaya da Paul Obor, an mika su ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ranar Juma’a a Lokoja tare da haramtattun kayan.
KARANTA WANNAN: INEC Za ta Tura Jami’ai 4k Domin Sake Zaben Kaduna – REC
Commodore Ugochukwu Ajulu, Kwamandan NNS Lugard Lokoja, a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin, ya bayyana cewa haramtattun kayan na dauke ne a cikin wata mota kirar Honda Accord saloon dake jigilar su daga jihar Edo zuwa Garki, Abuja, domin kasuwanci.
A cewarsa, wadanda ake zargin ‘yan asalin jihar Binuwai ne, an kama su ne a yayin aikin sintiri da sojojin ruwa suka yi a hanyar Ajaokuta zuwa Lokoja ranar Talata.
Ya bayyana cewa, “Muna nan a NNS Lugard Lokoja domin mika masu laifin biyu da haramtattun abubuwa masu nauyin kilogiram 400, gami da mota kirar Honda saloon ga jami’an NDLEA domin gurfanar da su gaban kotun shari’a.
Ajulu ya ce, shingayen binciken sojojin ruwa da ke Kogi sun yi aiki a bisa umarnin da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla ya ba su.
Jami’in hukumar NDLEA dake kula da reshen jihar Kogi, Sufuritanda mai kula da harkokin muggan kwayoyi, Olorunfemi Abolarinwa, ya ce za a bincike su da kyau kafin a gurfanar da su gaban kuliya domin su zama masu hana wasu.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Super Eagles Ta Lallasa Kamaru Da Ci 2-0
Yanzu haka dai Najeriya ta lallasa Kamaru da ci 2-0 a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2024
‘Yan wasan na Super Eagles suna da babban kalubale a gaban su inda za su kara da Angola a wasan kusa da na karshe
Tuni dai ‘yan Najeriya suka barke da murna kan wannan Nasara ta Super Eagles
Yanzu haka dai Najeriya ta lallasa Kamaru da ci 2-0 a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2024 da suka fafata a yau Asabar
Ademola Lookman ne ya zura kwallaye biyu a kowane rabin lokaci inda Najeriya ta samu nasara a kan Indomitable Lions.