Hukumar FRSC ta Chafke Ɓarawon Mota, a yayin da yake ƙoƙarin chanja Takardun Mallaka
Hukumar kiyaye haddura ta ƙasa FRSC ta kwato Motar da aka sace, inda ta kama wasu da ake zargin ɓarayin ne a lokacin da suke ƙoƙarin yin canjin Takardun motar zuwa mallakin su.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC reshen Jihar Abia ta kama wani da ake zargin barawon mota ne a garin Aba tare da kwato wata motar sata.
Mataimakin Kwamandan kula da harkokin Jama’a na Hukumar FRSC a Abia Chinwendu Enyioko ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Enyioko ya ce an gano motar Toyota Camry da aka sace mai lamba URL 974 TY a garin Aba ta hanyar tsarin tantance motoci na ƙasa da Hukumar FRSC ke yi.
KARANTA WANNAN LABARIN:An Cafke Soja Mai Ritaya da Farar Hula Dauke da Haramtattun Kayayyaki
Mataimakin kwamandan ya ƙara da cewa an gano motar ne a lokacin da wanda ake zargin ya kawo motar ga Jami’in Hukumarar FRSC da ke garin Aba domin samun canjin mallaka, inda ya bayyana cewa an miƙa wanda ake zargin da motar da aka sace ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.
Jami’in kula da ilimin jama’a na FRSC ya shawarci al’umma da su yi Rijistar Motocinsu akan tsarin tantance ababen hawa na ƙasa, inda ya ce an kwato motoci takwas a cikin shekaru biyu da suka gabata ta hannun hukumar NVIS.
Mataimakin kwamandan ya ƙara wayar da kan al’umma cewa rajistar motoci a Hukumar ta NVIS tana baiwa hukumomin tsaro a ƙasar nan bayanan sirri masu amfani.
A wani labarin kuma:danKakakin Majalissar da aka tsige ya Garzaya zuwa kotu
Kakakin Majalissar da ake tsige ya Garzaya kotu
Kakakin Majalissa Oluomo wanda aka tsige a Ogun ya garzaya kotu.
Tsohon kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ogun Olakunle Oluomo ya ce ya shigar da kara a gaban Babbar Kotun Jihar yana kalubalantar tsige shi da aka yi.
Olakunle ya magantu ne akan shigewar bayan da wata gidan Jarida ta bayar da rahoton rashin mayar da martani da kuma ƙin yin tsokaci kwanaki uku da tsige shi ba zato ba tsammani a matsayin Shugaban Majalisar.