Iyalan tsohuwar shugabar Matan Jam’iyyar PDP ta Jihar Kogi Misis Salome Acheju Abuh da aka banka mata wuta da ran ta a babban zaben da ya gudana a Jihar a shekara ta 2019 sun bukaci da a biya su diyya tare da yi musu adalci.
Mijin Misis Salome mai suna Elder Simeon Abuh wanda suka yi jerin gwano da ƴayan shi gaban yan jarida a birnin tarayya Abuja, sun bukaci gwamnatin tarayya da manyan kungiyoyi duniya da su sanya baki a maido muau da gidan su da aka kona kurmus.
Ya ce tun bayan da wasu yan barandar siyasa suka kone gidan kurmus wanda ya kunshi bangare mai dakuna biyar da dakuna hudu da kuma wani sashwn mai dakuna biyu al’amurra suka sukurkuce musu ba sa iya gane komai.
Ya ce lallai duniya abar tsoro ce, domin tun bayan da lamarin ya auku babu wani da ya yi hobasa kama daga gwamnati ko wata jam’iyyar siyasa da ma ita kan ta PDP da suka kawo wani doki.
Elder Abuh ya jaddada wa gwamnati irin halin da sukw ciki inda ya ce lallai ya kamata ta tura wata tawaga ta musamman da za ta duba lamarin don ceto su daga halin rugujewa.
Daga bisani ya mika kokon barar su ga jami’an yan sanda da su tabbatar da cewa sun bankado duk wani mai hannu cikin aika-aikar don girbe abinda suka shuka.