Yan bindiga da suka yi garkuwa da daliban Jami’ar Greenfield dake garin Kasarani na karamar hukumar Chikun dake Jihar Kaduna sun kashe uku daga cikin daliban.
A ranar talata ne dai wasu gungun yan bindiga suka yi awun gaba da da daliban jami’ar da wasu Malamansu bayan da suka yi musu dirar mikiya a talatainin dare.
Bayan da suka yi garkuwa da mutanen, daga bisani sun bukaci da a biya su naira miliyan dari takwas a matsayin kudin fansa gabannin su sake su.
Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar da cewa an gano gawarwakin daliban ne baki da hanci da jami’ar a yau juma’a.
Kawo yanzu dai babu wani karin bayani dangane da sauran daliban da kuma malaman su.
Idan za a iya tunawa dai Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir el-Rufa’i ya sha alwashin cewa gwamnatin sa ba za ta yi wata zaman sulhu da yan bindiga ba.