Kasar Malawi dake arewacin Afirka ta ce Allanbaram sai ta lalata Allurar Rigafin Korona na Kamfanin AstraZeneca kimanin dubu goma sha shida duk Gargadin da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi mata kan hakan.
A Farkon watan Maris din da ya gabata ne dai kasar ta karbi allurar guda dubu dari uku da sittin, to sai dai daga bisani ya fahimci cewa wa’adin daina aikin shi zai kare gabannin a ce ta gama sokawa wa kowa.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce za a iya Amfani da allurar Rigafin har na tsawo watanni talatin da shida daga ranar da aka sarrafa ta, don haka ne ya sa ta shawarci kasashen Afirka da su adana har sai an musu karin bayani.
To sai dai Ma’aikatar Lafiyar Kasar Malawi ta bakin kakakin ta Joshua Malango ta ce atafau ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa, don haka bata ga wanda zai hana lalata allurar ba saboda wanda aka bata tuni wa’adinta ya kusa cika.
Kazalika Ma’aikatar ta ce baya ga karewar wa’adin rigafin, wani dalili da zai sa dole sai ta lalata shi shine yadda yan kasar ke dar-dar na cewa su fah ba za a yi musu wannan allurar ba sai dai a chanja wata.
Idan aka yi jimillar allurar da za a lalata a Nahiyar Afirka tsakanin kasar Malawai da Sudan ta Kudu kawai adadin zai haura dubu saba’in a halin da ake ciki.