Kasa da mako guda Kenan bayan da aka tsinci wani jariri a unguwar Bako dake karamar hukumar Kwali na birnin tarayya Abuja, yanzu an sake gamdakatar da wani jaririn sabon haihuwa da uwar sa ta jefar da shi a Unguwar rukunin gidaje na Pegi dake karamar hukumar Kuje duk a birnin tarayya Abujan.
Wani Mazaunin unguwar mai suna Mista Kazeem Adeyemo wanda ya tsinci jaririya, ya ce abin bakin ciki sun gaza ceto rayuwar ta bayan da ta yi bankwana da duniya a asibitin da aka kaishi a nan Abuja.
Ya ce al’amarin ya faru ne a daren ranar juma’a wuraren karfe uku bayan da ya tashi yin Nafilar dare a dai wannan unguwa ta Rukunin gidaje na Pegi, nan ya ji wata sabuwar murya da bai saba ji ba a talatainin dare ta tagar gidan ahi, kum bai yi wata-wata ba nan takee ya fita dubawa sai ya tarar da cewa jaririya ce.
Ya ce baya da ya sanar da Makwabtan shi dangane sa wannan bakon al’amari, kazalika ya Tuntubi yan sanda inda daga bisani yam sandar ne suka garzaya da ita zuwa babban asibitin Kuje.
Ya kara da cewa abin takaici shine yadda kayan aiki a asibitin ya yi ƙaranci ta inda aka gaza ceto rayuwar yarinyar bayan da take bukatar kulawar gaggawa.
Kakakin Rundunar Yan Sandar birnin tarayya Abuja Maryam Yusuf ta gaza amsa kiraye-kiraye da Jaridar Daily Trust ta yi mata, kana a hannu guda ma ba ta amsa sakon kar-ta-kwana da aka aike mata ba.
Idan za a iya tunawa dai a Ranar Alhamis din da ta gabata ma an tsinci wani jariri a Shataletalen Airport dake Abuja inda aka cire mishi mukamuk, kuma ana zargin yan kungiyar asiri ne suka sace shi.