Babban Kamfanin Man nanna Kasar Faransa Total ya dakatar da aikin dashen makamashin iskar gas da yake yi a Kasar Mozambique, yan makonni bayan da yan tawaye suka kai hari wani kauye dake kusa da inda ake aikin.
Kamfanin ya ce da wannan kuma zai janye dukkanin ma’aikatan shi daga yankin domin ba zai iya sanya su cikin haɗari ba.
Gwamman Mutane ne dai suka rasa rayukansu a yankin Palma dake makwabtaka da inda ake aiki kuma gurin da harin ya auku a watan Maris din da ya gabata.
Wannan Katafaren aiki da kamfanin ke yi da kudin sa ya kai dala biliyan ashirin, shine aiko mafi girma da yake yi a nahiyar Afirka.
Masana’antar dake Afungi kusa da kauyen Palma na ci gaba da fuskantar kai hare-hare a yan baya-bayan nan, lamarin da ake dangantawa da Kungiyar IS.
To sai dai shugaban kasar ta Mozambique Felipe Nyusi ya sha alwashin maido da doka da oda a yankin.