Wani dan Najeriya mazaunin kasar waje ya bayyana alwashinsa na gamawa da kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa bayan da ya ware zunzurutun kusinsa ya sayi tankar yaki.
Lamarin mutumin ya ja hankalin jama’a da dama a kafafen sada zumuntar zamani bayan da ya wallafa wannan alwashi nashi.
Mutumin wanda ya ce ya sayi tankar yakin ne da niyyar Murkushe tsagerun Boko Haram, ya ce ba su kadai ba ma dum miyagun ayyuka a kasar nan sai ya ga bayansu.
A faifan bidiyon da ya wallafa, ya nuna yadda yake tsaye a gefen tankar inda yake shan alwashin cewa dole ne ya dawo Najeriya ya shiga Sambisa don gamawa da kungiyar ta Boko Haram.
Mutumin wanda har yanzu ba a iya tantance ko shi wanene ba ne, ya ce tankar za ta iso Najeriya nan da makonni hudu, kuma babu bata lokaci zai yi dirar mikiya a dajin na Sambisa.