Kocin Ƙungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel ya tsawaita zamansa a Ƙungiyar har zuwa 2024.
A watan Janairun Wannan shekara ne Tuchel mai shekara 47 ya haɗe da Chelsea a kwangilar watanni 18 bayan da ya maye gurbin Frank Lampard.
Kazalika Tuchel ya jagoranci Chelsea lashe gasar zakarun turai ta Champions League, yayin da kuma Ƙungiyar har wa yau ta kammala gasar Firimiya a mataki na huɗu.
Idan za a iya tunawa Tuchel ya karɓi ragamar Chelsea ne sa’ilin tana mataki na tara a gasar ta Firimiya, amma cikin kankanin lokaci ya jagorance ta zuwa wannan gagarumar nasara.
Thomas Tuchel shine koci ka farko da ya kai ga wasan karshe a gasar zakarun turai da kungiyoyi daban-daban, a shekarar 2020 ne ya jagoranci PSG inda ta sha kashi hannu Bayern Munich.